Ko Solskjaer zai kai bantensa a United?

Premier

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Laraba ne Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a kwantan gasar Premier mako na 31 da ya kamata su fafata tun 16 ga watan Maris.

Sai dai kuma ko yaya United za ta yi karawar ganin cewar an doke ta wasa shida daga takwas da ta yi a baya bayan nan?

A ranar 28 ga watan Maris ne Manchester United ta nada Ole Gunnar Solskjaer matsayin kocin din-din-din, bayan da ya ci wasa 14 daga 17 a matakin rikon kwarya.

Daga baya ne Solskjaer ya yi rashin nasara a hannun Arsenal da kuma Wolverhampton, jumulla rashin nasara a karawa shida cikin wasa takwas, ciki har da 4-0 da Everton ta doke ta.

Manchester United tana mataki na shida da maki 64 a kan teburin Premier.

Asalin hoton, BBC Sport

Ga jerin wasannin da Manchester United ta yi mafi muni a tarihi.

  • Rabon da United ta yi rashin nasara a wasanni a kankanin lokaci shi ne tsakanin Afirilu zuwa Mayun 1989, inda aka doke ta wasa shida daga bakwai da ta yi.

Kungiyoyin da suka yi nasara a kan United a lokacin sun hada da Derby da Charlton da kuma Coventry, sai ta ci Wimbledon daga nan kuma Southampton da QPR da kuma Everton suka yi nasara a kanta.

  • Red Devils ta yi rashin nasara a karawa biyar a jere a wasannin waje, tarihi mafi muni tun wanda aka ci fafatawa shida a jere a waje tsakanin Janairu zuwa Maris din 1981.

Kungiyoyin da suka yi nasara sun hada da Nottingham Forest da Sunderland da Coventry da Leicester da Manchester City da kuma Southampton a wancan lokacin.

  • Rabon da United ta yi rashin nasara a karawa bakwai daga wasa tara tun Satumba zuwa Oktoban 1962, inda ta yi rashin nasara a gidan Bolton da Leyton Orient.

Daga baya ne kungiyar ta doke Wanderers a Old Trafford, sai kuma ta yi rashin nasara a hannun City da Burnley da Sheffield Wednesday da Blackburn da kuma Tottenham, sai canjaras da Blackpool.

  • Red Devils ta yi wasa 11 kwallo na shiga ragarta a karon farko tun bayan 1998 a lokacin da Solskjaer ke buga wa kungiyar tamaula.
  • An ci United kwallo 48 a Premier shekarar nan, wannan ita ce kaka mafi muni da aka zura kwallaye da dama a ragar United, tun 45 da aka ci ta a kakar 1999-2000 da kuma 2001-02.
  • Idan har United ta yi rashin nasara a karawar da za ta yi da Manchster City da kuma Chelsea nan gaba zai zama karo na biyu da aka doke ta wasa hudu a jere a dukkan fafatawa.

An taba cin Red Devils wasa hudu a jere a Disambar 2015, inda Wolfsburg da Bournemouth da Norwich da kuma Stoke suka yi nasara a kanta.

Asalin hoton, Getty Images