Barcelona na dab da lashe kofin La liga

Jordi Alba da Clement Lenglet

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jordi Alba da Clement Lenglet ne suka ci wa Barcelona kwallo a ragar Sociedad

Barcelona na dab da lashe kofin La liga karo na takwas a shekaru 11 bayan ta doke Real Sociedad 2-1.

Barcelona ta ba Atletico Madrid tazarar maki 9 da ke matsayi na biyu a tebur, inda yanzu Barca ke neman maki shida kawai ta sake kare kofinta na La liga.

Nasarar da Barcelona ta samu na nufin za ta iya lashe kofin gasar a karshen mako idan ta doke Alaves a ranar Talata da kuma Levente a ranar Asabar.

Barca na kuma iya lashe kofin na La liga tun a tsakiyar mako idan ta doke Alaves kuma Atletico Madrid ta sha kashi a hannun Valencia a ranar Laraba.

Lashe kofin a karshen mako zai ba Barcelona lokaci sosai da za ta shirya wa haduwarta da Liverpool a gasar zakarun Turai zagayen dab da karshe, yayin da kuma alamu ya nuna Liverpool za ta ci gaba da yakin lashe kofin Premier tsakaninta da Manchester City har zuwa karshe wasannin gasar.