Juventus ta lashe kofin Seria A sau takwas a jere

Juventus' Cristiano Ronaldo (left) and Alex Sandro

Asalin hoton, Reuters

Cristiano Ronaldo ya ce zai ci gaba da taka leda a Juventus bayan kulub din ya lashe kofin Seria A karo na takwas a jere.

Juventus ta lashe kofin ne bayan ta doke Fiorentina 2-1.

Ronaldo wanda Juventus ta karbo daga Real Madrid kan fam miliyan 99.2, yanzu shi ne dan wasa na farko a tarihi da ya lashe Lig a Ingila da Spain da kuma Italiya bayan ya taimakawa Juventus lashe kofin Seria A na 35 da kungiyar ta lashe a tarihi.

Ronaldo ya ce ya yi farin cikin lashe kofin Seria A a kakarsa ta farko, duk da cewa an fitar da shi daga gasar zakarun Turai.

Asalin hoton, Twitter

Ajax ce ta fitar da Juventus daga gasar zakarun Turai, amma Ronaldo ya ce badi na nan.

Tun 2011 Juve ke lashe kofin Seria A bayan ta koma filin wasanta Allianz Stadium.