Ole Gunnar Solskjaer: 'Akwai kwayoyin halittar DNA na Man Utd a jinin 'yan wasana'

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United ba ta kai wani hari mai muni ba sai a minti na 86 a karawarsu da Everton

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce yawancin 'yan wasansa suna dauke da kwayoyin halittar DNA na kungiyar bayan da kungiyar Everton ta doke ta.

United ta yi rashin nasara da ci 4-0 a ranar Lahadi kuma wannan ne wasa na shida da ta yi rashin nasara a wasanni shida cikin wasanni takwas da ta buga.

Dan wasan gaban kungiyar, Paul Pogba, ya ce takwarorinsa 'yan wasa "ba sa daraja kungiyar ko magoya bayanta" lokacin da suka yi rashin nasara.

"Za ka fahimci 'yan wasa ne. Yanzu ba lokaci ba ne na yin sauyi gaba daya," in ji Solskjaer a ranar Talata.

"Za ka iya ganin kwayoyin halittar DNA a jikin yawancin 'yan wasan nan. Ya kamata a shigo da wasu 'yan wasa, mu kuma cire wasu."

United tana mataki na shida ne a teburin gasar firimiya kuma ba za ta samu damar zuwa gasar Zakarun Turai ba idan ta kammala kakar bana a haka.

Solskjaer ya nemi gafarar magoya kungiyar bayan da Everton ta doke su, inda ya ce yana da kwarin gwiwa kan kungiyar za ta kai matakin da ake fata bayan tabbatar da shi a matsayin kocin kungiyar na dindindin a watan Maris.

"Ina da kwarin gwiwa a kaina da kuma kungiyar," ya ci gaba da cewa a shirye nake na fuskanci kalubale, na san cewa kalubalen babba ne. Wannan ne abin da ya sa na zo nan."

"Ba na kaunar rashin nasara a wasa, amma hakan babban kalubale," inji shi.