Man Utd v Man City: Ko zakarun 1999 za su iya ja da yaran Pep Guardiola?

Ole Gunnar Solksjaer da Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Babu shakka Manchester United ce kungiyar da za ta iya taka wa Manchester City burki a kokarin da take yi na cin kofi uku - na Firimiya da na FA da kuma na Lig.

Kungiyar Manchester United ce kadai ta taba lashe wadannan kofuna uku a kakar wasa daya - Firimiya Lig da Kofin FA da Kofin Zakarun Turai - wanda a yanzu ya zama abin tunkaho ga kungiyar.

Idan Manchester City ta doke United a Old Trafford a karawarsu ta ranar Laraba, nasarar za ta ba kungiyar Pep Guardiola karfin gwiwar kafa nasu tarihin na cin kofi uku da babu wata kungiyar Ingila da ta taba hada wa a kakar wasa daya a tarihin kwallon kafa.

To a wannan lokacin da kungiyoyin na Manchester biyu ke shirin fafatawa mai matukar muhimmanci, wannan ya kasance lokacin da ya fi dacewa mu kwatanta kungiyar United ta shekarar 1999 da City ta 2019, sannan mu duba 'yan wasan da ka iya samun shiga wata hadaddiyar kungiya ta 'yan wasa 11 na musamman daga kungiyoyin biyu.

Sauye-sauye a bangaren tsaron gida

Babu inda za ka iya ganin sauyi karara kamar a bangaren tsaron gida idan ka kwatanta shekarun 1990 da na yanzu.

Gasa ta farko da Peter Schmeichel ya lashe tare da Manchester United a 1993 ta zo bayan shekara daya da aka hana mai tsaron gida ko gola kama kwallo da dan wasan kungiyarsa ya mayar masa, wato "Back Pass", kuma a lokacin dansa Kasper na da shekara shida da haihuwa.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Ederson na iya lashe kofin Firimiya na biyu a kakar wasa biyu a jere, amma Peter Scmeichel ya lashe gasar sau biyar a kakar wasa takwas da yayi a Old Trafford

Yanzu masu tsaron gida sai dai su buga kwallo da kafarsu, kuma Kasper ya zama mutum mai shekara fiye da 30 da haihuwa, wanda shi kansa ya lashe gasar Firimiya da kungiyarsa. Rayuwa ke nan.

Bari mu duba Schmeichel da Ederson. Tsohon golan na United na da tarihin iya mika wa dan wasan kungiyarsa kwallo na kashi 48 cikin 100 a kakar wasa ta 1998-99, amma sai ya kama kwallo 99 a gasar Firimiya a shekarar inda United ta sha gaban Arsenal ta lashe gasar.

A bana kuwa Ederson ya mika kwallo kashi 78 cikin 100 ga dan wasan kungiyarsa wato kammalallen pass ke nan, amma sau 54 ya kama wa kungiyarsa ta City kwallo a gasar ta bana, kuma dan wasan, wanda dan Brazil ne, ya taimakawa 'yan kungiyarsa kwallayen "Assist" da aka ci kwallo da su fiye da Romelu Lukaku a gasar ta bana.

Tsaron baya: Ga abin da ya kamata a mayar da hankali a kai

Sai an zura wa Man City karin kwallaye 16 a ragarsu a wasanni hudu da suka rage masu a kakar wasa ta bana kafin su samu sakamakon da Man United ta samu a kakar wasa ta 1998/1999.

Duk da shahararrun 'yan wasan baya kamar Gary Neville da Jaap Stam da Dennis Irwin da kuma daya jerin na Ronny Johnsen da Henning Berg da Wes Brown har ma da David May, an zura wa United kwallaye uku har sau uku - daya a Arsenal, daya a Sheffield Wednesday sannan na karshe a gida lokacin da Middlesborough ta ziyarce ta.

Amma a bana, City sau daya aka zura ma ta kwallo uku, kuma sau uku aka taba cin City da kwalo uku tun 2017.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Benjamin Mendy

Wasan Tsakiya: Zakaru da shahararru

Kawo 'yan wasan tsakiya da suka fi na David Beckham da Roy Keane da Paul Scholes da kuma Ryan Giggs idan za ku iya.

A gasar Firimiya ta 1998/1999, wadannan 'yan wasan hudu kawai sun taimaka da cin kwalo "assist" 37 tsakaninsu, inda Nicky Butt ya samar da biyar shi kadai.

Amma City ma na da 'yan wasan tsakiya da suka goge. David Silva na da assist 21 fiye da wani dan wasa a gasar firimiya tun shekarun 2010.

Kevin de Bruyne ne kan gaba a bayar da assist a tarihin Firimiyar Ingila, Leroy Sane kuma ke bi masa a matsayi na biyu.

Amma David Beckham ya ci kwallo sau shida ta "Direct Free Kick" fiye da kowane dan wasa a tarihin gasar Firimiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarun 1990 David Beckham na buga wa Man United free kick abin sha'awa ne

Attack: Jaruman zura kwallo: De Bruyne zuwa ga Silva sai Yorke sai Cole… GOAL!

A karshen shekarun 1990, Manchester United na da zakarun 'yan wasa na gaba su hudu.

Su kuwa City su fi dogara da 'yan wasa kamar Raheem Sterling da Sergio Aguero.

Tamabaya a nan ita ce, ta yaya Guardiola zai yi amfani da Dwight Yorke da Andy Cole da Teddy Sheringham da kuma mutumin da zai kara da shi wato Ole Gunnar Solksjaer da zai sami dama?

Andy Cole ya zura kwallo 187 - shi ne ke kan gaba a jerin 'yan wasan da suka samu zura kwallo fiye da 100 (sauran su ne Les Ferdinand da Emile Heskey da Peter Crouch da Paul Scholes).

Amma Yorke ne ya kafa tarihin jefa kwallaye fiye da takwas ta amfani da kansa a kakar wasan Firimiya daban-daban.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sergio Aguero (19) da Raheem Sterling (17) na da kwallo 36 tsakaninsu a gasar Firimiyar bana

To mun fara duba wannan karawar mai zuwa da duba bambancin da ke tsakanin Scmeichel da Ederson, amma a wajen 'yan wasa na gaba, labarin ya fi sarkakiya.

Wace kungiya ce ta fi a ganinku? Daya dai ta lashe kofi uku, daya kuma na da wasanni kadan kafin ta iya samin damar kafa nata tarihin.

A kakar wasa ta 1998-99, Man City na buga wasanta ne a rukuni na uku na kwallon kafa a Ingila, kuma sun shefe shekara 10 ba su iya doke abokan adawarsu ba.

Lallai United na fuskantar kalubale, amma abubuwa ba su gama lalacewa ba tukuna.

Abin lura a nan shi ne a fagen kwallon kafa, babu kungiya mai dorewa na din-din-din face 'yan kwararun 'yan wasa.