Man Utd da City: 'Yan Liverpool sun jingine gaba

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja
'Yan Liverpool sun zama magoya bayan Manchester United na rana daya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Liverpool sun zama magoya bayan Manchester United na rana daya

Dimbin magoya bayan Liverpool sun ce a karon farko za su goyi bayan Manchester United a wasan da za ta fafata da Manchester City a gasar Premier.

Wasan zai ja hankali da ake ganin zai tantance wanda zai lashe kofin Premier na bana tsakanin Liverpool da Manchester City.

Tazarar maki biyu Liverpool ta ba Manchester City a teburin Premier, yayin da ya rage wasanni uku a kammala gasar.

Wasan dai kwante ne ga Manchester City wanda zai ba Guardiola damar darewa tebur idan ya doke Manchester United a Old Trafford.

Yawancin 'yan wasa da magoya bayan Liverpool sun ce wannan ne karon farko da za su goyi bayan Manchester United a wani wasa.

Suna ganin United din ce za ta ba su nasarar lashe kofin Premier na bana idan har ta doke Manchester City ko ta rike ta kunnen doki.

Dan wasan Liverpool James Milner ya ce wannan ne karon farko a rayuwarsa da zai goyi bayan babbar abokiyar gaba Manchester United.

Sai dai dan wasan ya ce ba zai iya kallon wasan ba, yana mai cewa bata lokaci ne.

Wasu na ganin ya rage ga Manchester United ga wanda take son ya lashe kofin Premier na bana tsakanin manyan abokan gabarta guda biyu Liverpool da Manchester City.

Sai dai wasu na ganin 'Yan Manchester United ba za su taba son Liverpool ta lashe kofin Premier ba saboda girman gabar da ke tsakanin kungiyoyin biyu.

Wasu magoya bayan Manchester United sun ce sun fi kaunar Manchester City ta lashe kofin da ace Liverpool ce ta lashe saboda girman gabar da ke tsakaninsu.

Wani dan Liverpool kuma ya ce ba zai taba goyon bayan Manchester United ba duk da cewa yana matukar son City ta yi bari a Old Trafford.

Ana dai amfani da karawar da Manchester United za ta yi da Manchester City domin shammatar magoya bayan Liverpool musamman gabar da ke tsakaninsu da Manchester United.