Messi zai lashe Ballon d'Or na shida

Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Lionel Messi ya nuna a shirye yake ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta bana da ake kira Ballon d'Or wato ta 2019.

Kokarin da Messi ke yi a tamula a wannan kakar musamman kwallaye biyu da ya ci Liverpool a Champions League ya kawo karshen ce-ce kucen wa ya kamata ya karbi kyautar.

Messi kyaftin din Argentina ya taimakawa Barcelona lashe kofin La Liga na bana kuma na 26 jumulla, shi kansa na 10 ya dauka.

Sannan kuma shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar ta La Liga, inda kawo yanzu ya zura 34 a raga, kuma saura karawa bibiyu a kammala wasannin shekarar nan.

Barcelona ta kusan kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool 3-0 a wasan farko na daf da karshe ranar Laraba.

Barcelona ta ci kwallayen ta hannun Luis Suarez, tsohon dan wasan Liverpool, sannan Messi ya ci biyu a fafatawar kawo yanzu ya zura kwallaye 12 a Champions League, shi ne ke kan gaba.

A ranar Talata Barcelona za ta ziyarci Anfield, domin buga wasa na biyu na daf da karshe a kofin Zakarun Turai na Champions League.

Haka kuma Barcelona ta kai wasan karshe a Copa del Rey na bana, inda za ta kece raini da Valencia a cikin watan Mayu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Croatia da Real Madrid, Luca Modric ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2018, wato Ballon d'Or.

Modric shi ne ya lashe kyautar dan wasan da babu kamarsa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, wadda Faransa ta lashe.

Haka kuma shi ne wanda aka zaba a matakin dan kwallon da ya fi yin fice a nahiyar Turai a shekarar ta 2018.

Messi ya kafa tarihi da dama tun daga yawan buga wasa da cin kwallaye da lashe kofuna, zai kuma so ya ci Ballon d'Or na shida da zai zama shi ne kan gaba a yawan lashe kyautar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Cristiano Ronaldo dan kwallon tawagar Portugal mai taka-leda a Juventus yana da Ballon d'Or biyar biyar jumulla wanda ya lashe a 2008 da 2013 da 2014 da 2016 da kuma 2017, inda ya yi kan-kan-kan da Lionel Messi shima mai biyar da ya dauka a 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.