Manchester United za ta buga Europa a badi

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta tashi 1-1 a gidan Huddesfield Town a gasar cin kofin Premier, wasan mako na 37 da suka buga ranar Lahadi.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Scott McTominay minti takwas da fara tamaula, daga baya Huddesfield ta farke ta hannun Isaac Mbenza minti 15 da komawa zagaye na biyu.

Wannan ne karo na biyu da United ta tashi 1-1 a gasar Premier bana, tun bayan wanda ta yi a Old Trafford da Wolverhampton ranar 22 ga watan Satumba.

Da wannan sakamakon United ta yi wasa biyar ba tare da yin nasara ba, tarihi mafi muni tun karawa takwas ba ta ci wasa ba a lokacin Louis van Gaal tsakanin Nuwamba da Disambar 2015.

Haka kuma saura wasa daya ya rage a kammala Premier bana, United ba za ta iya tarar da Chelsea ko Tottenham ba, bayan da take ta shida biye da Arsenal wadda za ta yi wasa idan anjima.

Wannan na nufin Manchester United za ta buga gasar Europa a kakar badi kenan.

Manchester United za ta buga wasan karshe da Cardiff City wadda ita ma ta fadi daga gasar Premier da ake yi.

Huddesfied ita ce ta karshe a kasan teburi da tazarar maki 11, za kuma ta buga wasan karshe a gidan Southampton wadda ta kai bantenta.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Labarai masu alaka