Chelsea ta kusa samun gurbin Champions League

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea na daf da samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League ta badi, bayan da ta doke Watford 3-0 a ranar Lahadi.

Kungiyar ta Stamford Bridge wadda ta karbi bakuncin gasar Premier karawar mako na 37, ta ci kwallaye ta hannun Ruben Loftus-Cheek da David Luiz da kuma Gonzalo Higuain.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma ta ukun teburi, bayan da a ranar Asabar Bournemouth ta doke Tottenham 1-0.

Chelsea za ta kammala Premier bana a mataki ta ukun teburi idan ta yi nasara a wasan karshe da za ta ziyarci Leicester City ranar Lahadi.

Canjaras ma zai iya sa Chelsea ta kare cikin 'yan hudun farko a teburin shekarar nan, amma hakan zai dogara kan sakamakon wasannin karshe da za a rufe kakar bana.

Chelsea tana buga gasar Zakarun Turai ta Europa, inda ta je ta tashi 1-1 a gidan Frankfurt a makon jiya, kuma The Blues za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar Alhamis.

Labarai masu alaka