Karan battar Liverpool da Barcelona

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Barcelona ta ziyarci Anfield domin buga wasa na biyu na daf da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ta bana.

Duk wadda ta yi nasara za ta samu gurbin buga karawar karshe ranar 1 ga watan Yuni a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke Madrid.

Sai dai kuma Barcelona ta yi nasara a wasan farko da ci 3-0 a makon jiya a Camp Nou, inda Luis Suarez ya ci kwallo da kuma Messi wanda ya zuba biyu a raga.

Wasan yana da kalubale da dama, duk da cewar Liverpool za ta buga karawar babu Mohamed Salah da Roberto Fermino wadanda ke yin jinya.

Barcelona ta ci wasa biyu baya a Anfield, inda ta yi nasara da ci 1-3 a 2001 da kuma 2007, sai dai kuma a bana babu kungiyar da ta doke Liverpool a Anfield a Champions League.

Wasu batutuwa da ya kamata ku sani:

Barcelona ta yi nasara a wasa hudu baya da ta yi a Champions League, inda kwallo bai shiga ragarta ba a karawa uku, kuma ba a ci ta a kakar bana ba a gasar.

Kawo wannan lokacin, wasa daya aka ci Liverpool a Anfield a dukkan gumurzun da ta ke yi a bana, shi ne ranar 26 ga watan Satumbar 2018 a fafatawa da Chelsea a gasar League Cup.

Barcelona ta yi gumurzu hudu a Anfield ta yi rashin nasara a karawa daya da canjaras daya ta yi nasara a fafatawa biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan wasan da suka buga zagayen farko:

Liverpool: Alisson da Gomez da Matip da Van Dijk da Robertson da Fabinho da Milner da Keita da Wijnaldum da Mane da kuma Salah.

Barcelona: Ter Stegen da Roberto da Pique da Lenglet da Alba da Busquets da Rakitic da Vidal da Coutinho da Messi da kuma Suarez.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan Barcelona 23 da suka je Anfield:

Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fuskanci Liverpool a Anfield a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League.

Sun hada da Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Coutinho da Arthur da Suarez da kuma Messi.

Sauran sun hada da Cillessen da Malcom da Lenglet da Murillo da Jordi Alba da Prince da Roberto da Vidal da Umtiti da Vermaelen da Alena da Inaki Pena da Wague, inda Rafinha ba zai buga wasan ba.

Labarai masu alaka