Bacelona ta leko ta koma a Champions League

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Liverpool ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Barcelona 4-0 ranar Talata a Anfield.

Liverpool ta ci kwallaye biyu ta hannun Divock Origi, sannan shima Georginio Wijnaldum ya ci biyu a karawar.

Barcelona ce ta ci 3-0 a makon jiya a Nou Camp, amma Liverpool ta zare su sannan ta kara daya a raga, inda ta kai wasan karshe da kwallo 4-3.

Da wannan nasarar da Liverpool ta samu za ta buga wasan karshe karo na biyu, za kuma ta fafata da wadda ta yi nasara tsakanin Ajax ko Tottenham a Madrid ranar 1 dga watan Yuni.

Wannan namijin kokarin da Liverpool ta yi ya yi irin kwazon da ta yi a kan AC Milan a 2005 da kuma doke Borussia Dortmund 4-3 a Anfield shekara uku da ta wuce.

Kawo wannan lokacin, wasa daya aka ci Liverpool a Anfield a dukkan gumurzun da ta ke yi a bana, shi ne ranar 26 ga watan Satumbar 2018 a fafatawa da Chelsea a gasar League Cup.

Liverpool tana ta biyu a teburin Premier, za ta buga wasan karshe da Wolverhampton ranar Lahadi.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Labarai masu alaka