Dalilai shida da aka ci Barcelona a Anfield

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tuni Liverpool ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ranar Talata, bayan da ta doke Barcelona a Anfield 4-0, jumulla 4-3.

Fitar da Barcelona a zagayen daf da karshe ya sa wasu na nuna wa koci yatsa da cewar shi ne ya tafka kurakuren da suka kai kungiyar ta Camp Nou ta yi ban kwana da gasar bana.

Sai dai kuma wasu na hange rashin kokarin wasu daga cikin 'yan wasan Barcelona a Anfield da suka hada da Jordi Alba da Marc-Andre Ter Stegen da Luis Suarez da kuma Philippe Coutinho.

1. 'Yan wasa 11 da suka fara karawar farko a Camp Nou.

Daman abinda ya kamata Barcelona ta yi shi ne ta fara wasa da wadanda suka ci mata kwallaye 3-0 a Camp Nou, kuma hakan ta yi.

Sai dai kuma ko a can Spaniya Liverpool ta taka rawar gani, inda ta kai hare-hare masu zafi amma kwallo bai shiga raga ba.

Kuma salon da Jurgen Klopp ya taka ya fi na Barcelona a Spaniya, kuma a Ingila ma sai ya fara da wani salon na daban tun da babu Mohamed Salah da Roberto Firmino.

Barcelona: Ter Stegen da Roberto da Pique da Lenglet da Alba da Busquets da Rakitic da Vidal da Coutinho da Messi da kuma Suarez.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

2.. Coutinho bai taka rawar da ta dace ba

Coutinho kamar yadda aka dauka zai sa matsi musamman karawa da tsohuwar kungiyarsa kuma a Anfield, sai aka kasa ganin haka, har ma wasu ke cewa bai kamata koci ya sa Coutinho a fafatawar ba.

Sai dai kuma Ousmane Dembele na jinya, kuma har yanzu Malcom bai samu gurbin shiga cikin 'yan wasan Barcelona kai tsaye ba, amma dai Coutinho bai taka rawar da ta dace ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

3. Canjin da Barcelona ta yi bai tsinana komai ba

Abin da ya bayar da mamaki shi ne 'yan wasan da suka fara gumurzun farko mako daya sune dai suka buga a Anfield, to amma mai ya sa suka kasa cin Liverpool ko da kwallo daya ne?

Kuma canji da kocin Barcelona ya yi a Spaniya a karawar farko shi ne dai ya yi a Ingila, inda Arthur Melo ya canji Arturo Vidal, shi kuwa Nelson Semedo ya maye gurbin Coutinho, sannan aka sa Malcon daga karshe amma duk bata sauya zani ba.

4. Koci ya yi kuskure wajen canji

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Valverde ya fitar da Vidal daga fili a minti na 74, kuma dan wasan tawagar Chile shi ne kadai dan kwallon da bai da katin gargadi, kuma yana taka tsantsan wajen tare da kwace kwallo da yin laifi.

Yayin da a lokacin Sergio Busquets da kuma Ivan Rakitic sai kara kaina suke yi a cikin fili, sai kawai aka fitar da Vidal.

5. Messi kamar baya cikin fili

Lionel Messi wanda ya zura kwallaye biyu a wasan farko a Spaniya, ya kasa nuna kansa a Anfield, inda kwallo 35 ya bayar a gabaki dayan wasan, inda ya buga kwallo shida da ta nufi raga.

'Yan wasan Liverpool sun kwan da sanin cewar sarari da suka bai wa dan kwallon Argentina a wasan farko shi ne ya samu damar da ya raunata su, saboda haka ba su bari ya wataya ba a Ingila, inda sau 17 suna kwace kwallo ko kuma hana shi abin da ya so yi da tamaula.

Kuma 'yan kwallon Liverpool din ba su yi laifi da yawa ba wajen kwace kwallo a wajen Messi da zai zamar musu matsala, don bai samu damarmaki a da'irar filin Anfield ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Messi shi ne dan wasan Barcelona da ke buga mata kwallo kai tsaye zuwa raga, ya kuma yi iya kokarinsa amma babu labari.

Rabon da Messi ya ci kwallo a waje a wasan daf da karshe tun wadda ya zura a ragar Real Madrid a 2010/11.

Ranar Talata a Anfield ba ta zama ranar Lionel Messi ba da 'yan wasan Barcelona da dama, kuma za a dade ba a manta namijin kokarin da Liverpool ta yi.

Wasannin da Barcelona ba ta ji da dadi ba a waje

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

6. Barcelona ta shiga matsi, minti 20 ya rage ta saka Arthur

Liverpool ta kai hare-hare da dama tun fara wasa ta dunga sawa Barcelona matsi ta kowanne bangare hagu da dama, inda Vidal ya kasa yin komai sai ma ya dunga barar da kwallaye cikin sauki, a wasan farko ma haka ya dinga yi.

Barcelona ta dauki Arthur don magance irin wannan matsalar idan an saka ta cikin matsi, amma sai a minti 74 Valverde ya saka dan kwallon a lokacin da sauran 'yan Barca ba su da laka a jiki.

Shin kuna ganin da wasu kurakuren da Barcelona ta yi a Anfield da ya kai Liverpool ta fitar da ita a Champions League?

Labarai masu alaka