Fifa ta yi watsi da daukaka karar Chelsea

Bertrand Traore holding a Chelsea shirt after signing in 2014 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarri ya ce kungiyar tana bukatar sayen 'yan wasa biyu a wannan kakar

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ce "ba abu ba ne mai sauki" ka kalubalanci Liverpool da Manchester City a kaka mai zuwa, bayan kungiyarsa ta yi rashin nasara kan batun dakatar da ita daga sayen sabbin 'yan wasa.

An haramta wa Chelsea sayen sabbin 'yan wasa idan aka bude kasuwar saye da musayar 'yan wasa guda biyu da ke tafe.

Hukuncin ya biyo bayan wani bincike kan 'yan wasa 'yan kasa da shekara 18 da kungiyar ta saya.

Chelsea ta ce "ba ta ji dadin hukuncin ba" kuma za ta sake daukaka kara zuwa kotun da ke sauraron kararrakin wasanni wato Court of Arbitration for Sport.

"Yana da wahala mu iya cike gibin a yanzu, ya kamata mu yi aiki tukuru, muna mukatar wani abu daga kasuwar saye da musayar 'yan wasa," in ji Sarri.

"Ba abu ba ne mai sauki, saboda kasancewa a matsayi na biyu, yana da wuya."

Sarri ya ce kungiyar tana bukatar sayen 'yan wasa biyu a wannan kakar.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba