Abubuwan mamaki a Champions League na bana

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gasar Champions League ta bana ta kai karawar karshe da za a yi ranar 1 ga watan Yuni a Madrid, inda za a kece raini tsakanin Liverpool da Tottenham.

Gasar bana an yi abubuwan ban mamaki kama daga fitar da manyan kungiyoyi da kasa taka rawar gani ga wasu fitattun 'yan kwallo da amfani da na'urar taimakawa alkalin tamaula yanke hukunci da dai sauransu.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ya yi nazari kan yadda gasar ta bana ta zama daban a tarihi:

Kungiyar Liverpool da Ajax da Tottenham da Manchester United da kuma Juventus sun nuna cewar komai zai iya faruwa a kwallon kafa.

A gasar bana ba za a manta da kungiyoyin da aka ci wasan farko da ake ganin an gama da su, amma da an zo karawa ta biyu sai su yi abin bajintar da babu wanda zai ce hakan zai faru ba.

Ga jerin abubuwan ban mamaki da aka yi a Champions League na bana:

1. Yadda Liverpool ta hana Barcelona kai wa zagayen karshe

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Misali na farko a fagen tamaula da ke nuna cewar komai zai iya faruwa a kwallon kafa shi ne yadda Liverpool ta fitar da Barcelona a wasan daf da karshe karo na biyu a Anfield.

Barcelona ce ta fara cin Liverpool 3-0 a Anfield, inda Luis Suarez ya fara cin kwallo sannan Lionel Messi ya ci biyu a wasan.

Mako daya tsakani Barcelona ta ziyarci Anfield, kuma Liverpool din ta buga karawar ba tare da Mohamed Salah da Firmino ba, sakamakon jinya da suke yi.

Hakan bai tashin hankalin 'yan wasan Liverpool ba, wadanda suka dinga kai wa Barcelona hare-hare ta ko ina hagu da dama sama da kasa har sai da Georgino Wijnaldum da kuma Divock Origi kowanne ya ci kwallo bibbiyu.

Kuma ba cin kwallaye hudun ba, har da hana Lionel Messi motsawa a fili kamar yadda ya saba, da hana Luis Suarez sukuni da sauran fitattun 'yan kwallon Barca.

Bajintar da Liverpool ta yi a ranar Talata, ita ce ta biyu mai abin mamaki, bayan wadda Barcelona ta yi nasara a kan Paris St Germain 6-1 gida da waje a 2016/17 a gasar.

2. Ajax ta kawo karshen lashe kofi uku a jere da Real Madrid ta yi

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ajax ce ta fara yin abin mamaki a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana, bayan da Real Madrid ta doke ta 2-1 a Netherlands, ita kuma ta je Santiago Bernabeu ta ci 4-1.

Kwallayen da David Neres da Dusan Tadic da Hakim Ziyech da kuma Lasse Schone suka ci, sune suka kawo karshen lashe kofi uku da Madrid ta yi a jere, kuma kwallaye da dama da aka ci kungiyar a gida a tarihin Champions League.

3. Ronaldo ya yi waje da Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Atletico Madrid ta yi nasara a kan Juventus da ci 2-0 a wasan farko, kuma hakan ne ya bai wa kungiyar kwarin gwiwar zuwa Turin da nufin za ta kai zagayen gaba.

Da aka fara wasa kai kace Juventus ba za ta taka rawa ba, sai kawai Cristiano Ronaldo ya nuna kwarewarsa da kuma nuna cewar ya san yadda ake cin kungiyoyin Spaniya, inda ya ci su kwallaye uku rigis shi kadai.

Cin da Ronado ya yi musu a karawar daf da na kusa da na karshe ya batawa 'yan Atletico rai matuka, domin ya hana kungiyar damar buga wasan karshe da za a yi a filinta ranar 1 ga watan Yuni.

4. Man United ta fitar da PSG, duk da wasu 'yan wasanta na jinya

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Paris St Germain ta je Old Trafford ta doke Manchester United da ci 2-0, ta kuma taka rawar da kowa ke ganin babu tantama ta kai zagayen gaba.

Kafin United ta ziyarci PSG karawar zagaye na biyu 'yan wasanta kamar Paul Pogba da Nemanja Matic da Ander Herrera da Anthony Martial da Phil Jones da Jesse Lingard da Matteo Darmian da Juan Mata da Alexis Sanchez da kuma Antonio Valencia.

United ta fara cin kwallo ta hannun Romelu Lukaku a farko-farkon take tamaula daga karshe ma suka tashi 3-1, inda Marcus Rashford ya ci ta karshe a bugun fenariti.

5. Porto ta yi waje da Roma

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Porto ta Portugal ta yi rashin nasara da ci 2-1 a Italiya a hannun Roma, hakan ya sa ta kwan da sanin sai ta doke kungiyar Italiya a filin wasa na Estadio Do Dragao idan tana son kai wa zagayen gaba.

Hakan kuwa aka yi inmda ta yi nasara da ci 3-1, kuma Alex Telles ya ci mata kwallo na uku a bugun fenariti a minti na 117, wanda hakan ya sa ta fitar da Roma.

6. Ajax ta kara bajinta ta biyu a kan Juventus

Ajax ta kara yin gwaninta a wasa na biyu a gasar ta Zakarun Turai, inda ta yi waje road da Juventus wadda ta yi kunnen doki 1-1 a wasan farko a Amsterdam.

A wasa na biyu a Italiya, Ajax ta je ta tayar wa da Juventus da Ronaldo hankali, inda ta yi nasara da ci 2-1 tare da matasan 'yan kwallonta, kuma karon farko da ta kai daf da karshe tun bayan shekara 22.

7. Karon batta mai kayatarwa tsakanin Manchester City da Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A wasa na biyu na daf da na kusa da na karshe, Tottenham ta ziyarci Etihad da kwallo daya, sai dai minti hudu da take wasa Manchester City ta ci daya, kidaya ta fara da 1-1 kenan.

Can kuma sai Tottenham ta ci biyu ta hannun Heung-min Son, hakan ya sa City ta kara kwazo inda ita ma ta zura biyu a raga ta hannun Bernardo Silva da Raheem Sterling sannan kuma Sergio Aguero ya kara, wasa ya koma 4-2.

Haka dai Tottenham ta ci gaba da sa kwazo ba ta fidda rai ba, sai kuwa Fernando Llorente ya ci kwallon da har yanzu ake takaddama a kanta, inda wasu ke cewa da hannun ya ci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani abin ban mamaki Raheem Sterling ya zura kwallo a raga daf da za a tashi inda filin Etihad ya rude da murna, sai dai kuma na'urar nan mai taimakawa Alkalin wasa yanke hukuncin wato VAR ta ce an yi satar gida ba a karbi kwallon ba.

8. An yi gumurzu a Amsterdam da Tottenham ta kai labari

Ajax ta yi nasarar doke Tottenham 1-0 a wasan farko na daf da karshe a Ingila, kuma ana zuwa gidanta fafatawarta biyu ta zura kwallaye biyu ba tare da bata lokaci ba.

Haka dai aka ci gaba da wasa kai kace Ajax ce za ta kai wasan karshe, amma sai kociyan Tottenham ya fitar da Victor Wanyama ya maye gurbinsa da Fernando Llorente.

Liorente ya taka rawar gani, amma dai Lucas Moura shi ne ya zama gwani inda ya ci kwallo uku rigisda hakan ya kai Tottenham wasan karshe da za ta fafata da Liverpool a Madrid.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kwallaye ukun da Lukas Moura ya ci ya zama dan Brazil na farko da ya ci uku a wasan daf da karshe, kuma na biyar jumulla da suka yi wannan gwanintar idan ka hada da Alessandro Del Piero da Ivica Olic da Robert Lewandowski da kuma Cristiano Ronaldo.

Ba a wannan gasar aka fara yin abin ban mamaki ko gwaninta a tamaula ba, amma a Champions League na bana jerin abubuwan ban mamaki da bajintar da aka yi ya dara na kowacce gasar.

Shin ko za ka tuna wani abin ban mamaki da aka yi a Champions League kuwa?.

Labarai masu alaka