Arsenal ta kai wasan karshe a Europa

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kwallaye ukun da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci sun taimakawa Arsenal kai wa wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa League ta bana.

Arsenal ta yi nasarar doke Valancia 4-2 a Spaniya, jumulla 7-3 kenan gida da waje.

Tun farko Arsenal ce ta doke Valencia 3-1 a wasan farko a Emirates, a karawa ta biyu a Spaniya kuwa, Gunners ta ci kwallo ta hannun Alexandre Lacazette, sannan Aubameyang ya ci uku rigis.

Ita kuwa Valancia mai masaukin baki ta ci kwallo biyu ne ta hannun Kevin Gameiro wanda ya ci ta farko minti 11 da fara tamaula, sannan ya kara na biyu a minti na 58.

Arsenal wadda ta rasa gurbin shiga gasar Champions League a Premier ta samu damar zuwa gasar badi kai tsaye idan ta lashe kofin Europa na bana.

Za a buga wasan karshe ne ranar Laraba 29 ga watan Mayu.

Labarai masu alaka