Chelsea da Arsenal a wasan karshe a Europa League

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Eden hazard ne ya ci Chelsea kwallon karshe da ya bai wa kungiyar doke Eintrancht Frankfurk da ci 4-3 a bugun fenariti a wasa na biyu na daf da karhe a Europa League.

Hazard wanda ake hasashen ya buga wasansa na karshe a Chelsea, ya ci kwallonsa ne, bayan da mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga ya tare kwallon Hinteregger da kuma ta Goncalo Paciencia.

Tun farko Chelsea wadda ta karbi bakuncin Frankfurt sun tashi wasan a ranar Alhamis 1-1 har da karin lokaci, a wasan farko ma a makon jiya kunnen doki suka yi.

Chelsea za ta fafata da Arsenal a wasan karshe a Baku ranar 29 ga watan Mayu, kuma hakan na nufin kungiyoyin Ingila ne za su fafata a gasar Champions League ranar 1 ga watan Yuni a Madrid.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wannan ne karon farko da kungiyoyi hudu daga kasa daya za su buga gasar Champions League da ta Europa Cup a kaka guda.

Tottenham ta kai wasan karshe bayan da ta fitar da Ajax ranar Laraba, ita kuwa Liverpool waje ta yi da Barcelona ranar Talata.

Liverpool tana mataki na biyu a kan teburin Premier, yayin da Tottenham ta samu gurbin shiga gasar Champions League shekara mai zuwa.

Ita ma Chelsea ta samu gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ta badi, yayin da Arsenal za ta ci gaba da fafatawa a Europa League na kaka mai zuwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sai dai idan Gunners ta lashe wasan karshe da za ta kara da Chelsea, hakan zai bata damar buga Champions League na gaba kenan kai tsaye.

Kociyan Arsenal, Unai Emery yana da tarihin lashe kofin Europo uku da ya yi a Sevilla a shekarar 2013-14 da 2014-15 da kuma 2015-16.

Yadda kungiyoyin suka taka-leda

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Labarai masu alaka