Champions Laegue da Europa League: Kungiyoyin Ingila sun kafa tarihi a Turai

Son Heung-min, Mohamed Salah, Eden Hazard and Pierri-Emerick Aubameyang Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tottenham da Liverpool da Chelsea da Arsenal za su wakilci Ingila a gasar Turai guda biyu ta bana

Kungiyiyoin Ingila sun kafa tarihi a harkar kwallon kafar Turai bayan da hudu daga cikinsu suka kai wasan karshe a manyan gasar nahiyar.

Arsenal ta ci wasanta a Valencia yayin da ita kuma Chelsea ta doke Eintracht Frankfurt a ranar Alhamis, inda suka kai wasan karshe a gasar Europa League.

Kafin haka an yi karon-batta tsakanin Liverpool da Barcelona da kuma Tottenham da Ajax a gasar Champions League.

Wannan ne karon farko da aka samu kungiyoyi hudu daga kasa daya da suka kai wasan karshe a gasar biyu.

An taba samun 'yan Ingila da suka buga wasan karshe a gasar Europa ta 1971-1972, sai kuma a Champions League, inda Man United ta doke Chelsea a bugun fenareti a shekarar 2007-2008.

'Yan Spaniya sun biyu sun buga wasan karshe a Champions League ta 2015-2016, inda Real Madrid ta doke Atletico Madrid yayin da kuma kungiyar Sevilla ta ci kofin Europa League a shekarar.

"Gasar Premier Ingila mai zafi ce sosai kuma ita ce kan gaba a Turai baki daya," in ji kocin Chelsea Maurizio Sarri.

Arsenal da Chelsea za su gwabza a birnin Baku na kasar Azerbaijan - nisan mil 2,468 daga birnin Landan - a ranar 29 ga watan Mayu.

Arsenal na tsaka mai wuya game da gurbin shiga gasar Champions Laegue ta badi, domin idan ba ta ci kofin ba to babu ita a gasar.

Idan kuwa ta ci to za ta zama kungiyar Ingila ta biyar ke nan a gasar.

Ita kuwa Chelsea tuni ta samu gurbin shiga gasar bayan da ta kare a cikin 'yan hudun farko watoTop Four a turance.

Filin wasa na Baku yana iya daukar 'yan kallo 68,700 ne kawai.

Sai dai hukumar Uefa ta bai wa kowacce kunigya tikiti 6,000 ne kawai, abin da Arsenal ta bayyana "rashin jin dadinsa".

Ta kuma ce ta hakan ya ba ta wajen rabon tikitin ga magoya bayanta.

Su kuwa Tottenham da Liverpool za su fafata ne a birnin Madrid ranar 1 ga watan Yuni, yayin da su ma magoya bayansu ke fuskantar nasu matsalolin zuwa kallon wasan.

Farashin kujerar jirgin sama yana kai wa har fan £1,300, inda ake zargin wasu kamfanonin da "cin kazamar riba."

Wani karin tagomashi shi ne, kungiyoyin Premier ne za su kuma karawa a gasar Uefa Super Cup, wadda ake yi tsakanin wanda ya lashe Champions Laegue da wanda ya lashe Europa League.

Za a buga Uefa Super Cup din a watan Agusta a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.