Hazard ya ce tun tuni ya fada wa Chelsea yana son koma wa Real Madrid

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya baya sun rera masa wakar suna kiransa da ya ci gaba da zama a kungiyar

Eden Hazard ya kammala kakar Premier ta bakwai a Ingila a matsayin dan wasan Chelsea sannan kuma ya bayyana cewa ya sanar da kulob din sha'awarsa ta barin kungiyar.

"Na gama yanke hukunci kuma na fada wa kulob din makonni da suka gabata amma ba wai ni kadai abin ya shafa ba", kamar yadda Hazard ya bayyana bayan wasan da suka tashi 0-0 da Leicester City.

"Na so hakan ta faru da wuri amma ba ta faru ba. Har yanzu ina jira kamar yadda magoya baya ma suke jira."

Chelsea za ta buga gasar Zakarun Turai ta Champions League a kakar badi, amma hakan ba zai hana Hazard tafiya ba.

Dan shekara 28, har yanzu yana muradin sake fuskantar sabon kalubale a wata kungiyar daban.

Sai dai Real Madrid na bukatar ta fito da kudi don sayo shi daga Chelsea.

Hazard ya ce: "Muna da wasan karshe na Europa da za mu yi, daga nan sai na ga yadda za a yi.

"Ban taba kawar da hankalina ba yayin da nake taka leda. A kodayaushe ina kokarin mayar da hankali kan kwallo kawai, ba na tunanin halin da kulob din ke ciki. Burina kawai in ci wasa."

Rashin Hazard a Stamford Bridge ba karamar illa zai jawo ba kuma za a shiga wani hali.

Ya ci kwallo 16 a kakar bana sannan ya taimaka kai-tsaye wajen cin 15.

Hazard ya gaishe da magoya bayan Chelsea jim kadan bayan an tashi daga wasan da ya buga minti 20 kawai, bayan da Sarriu ya ajiye shi a benci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Su kuwa magoya baya suka yi ta rera masa wakar neman ya zauna a kungiyar. Sai dai bai jima ba a filin ya fice.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption "Akwai jinin Hazard a Chelsea kuma Chelsea gidanka ce", magoya bayan Chelsea suka rubuta a wannan kyallen

Tun farko kocin kungiyar Maurizio Sarri ya ce wajibi ne a girmama zabin dan wasan.

Ya lashe kyauta

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hazard ne ya ci kyautar Premier League Playmaker 2018/2019

Har wa yau, mintuna kadan bayan an tashi daga wasan aka bai wa Hazard kyautar dan wasan da ya fi kowa taimaka wa abokan wasansa wajen cin kwallo - Premier League Playmaker 2018/2019.

Dan wasan ya taimaka wajen cin kwallo 15 sama da Callum Wilson na Bournmouth da Paul Pogba na United masu tara kowannensu.

Sannan kuma ya zura kwallo 16 shi da kansa.

Labarai masu alaka