Barcelona za ta 'sayi' Antoine Griezmann

Kylian Mbappe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ranar Lahadi ne aka bai wa Mbappe kyautar zakakurin dan wasa mai tasowa a gasar Ligue 1 ta Faransa

Dan wasan Faransa, Kylian Mbappe, mai shekara 20, ya ce zai iya barin Paris St-Germain a kakar bana, wanda hakan ya sa manyan kungiyoyi kamar Real Madrid da Barcelona da kuma Manchester City fara zawarcinsa, in ji jaridar Express.

Za a bai wa kocin Manchester City Pep Guardiola damar ci gaba da jagorantar kungiyar har tsawon shekara biyar masu zuwa kuma zai rika samun fam miliyan 100 yayin da albashinsa zai karu daga fam miliyan 15 zuwa 20, in ji jaridar Sun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Guardiola ya lashe kofin Premier karo na biyu a jere

Manchester United tana duba yiwuwar kiran Alexis Sanchez, mai shekara 30, daga hutu don ya buga mata wasannin tunkarar kaka mai zuwa, kamar yadda jardar Sun ta bayyana.

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce sun fara zawarcin dan wasan Faransa Antoine Griezmann, bayan dan kwallon ya ce zai bar Atletico Madrid a bana, in ji jaridar Express.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Leicester City Harry Maguine, mai shekara 26, shi ne dan wasan da Guardiola yake sa ran zai maye gurbin Vincent Kompany wanda ya bar City a bana, a cewar jaridar Mail.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya nuna alamun cewa zaman dan wasan Wales Gareth Bale a kungiyar ya kusa karewa, in ji kafar yada labarai ta Eurosport.

Bale ya shaida wa abokan wasansa cewa yana fatan ganin karshen kwangilarsa a kungiyar kafin ya tafi, a cewar kafar (Radioestadio, via Mail).

Labarai masu alaka