Bayern Munich na neman Sane, Conte zai koma Inter Milan

Leroy Sane Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bayern Munich tana da kwarin gwiwar ci gaba da neman dan wasan Jamus Leroy Sane, mai shekara 23, daga Manchester City, a cewar jaridar Mirror.

Tsohon Kocin Chelsea Antonio Conte ya amince ya koma kungiyar Inter Milan a matsayin sabon kocinta a bana, a cewar jaridar Guardian.

Yayin da kungiyar Juventus ta dauke idonta a kan Conte kuma ta fara zawarcin Kocin Chelsea na yanzu wato Maurizio Sarri, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Manchester United za ta nemi a biya ta fam miliyan 138 kafin ta saki dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, kamar yadda jaridar Star ta bayyana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Har wa yau, United ta shirya fara zawarcin dan wasan Benfica Joao Felix wanda aka yi wa farashin fam miliyan 105, duk da cewa ita ma Real Madrid tana neman dan kwallon na Portugal, mai shekara 19, in ji kafar (Record, via Mirror).

Chelsea ta shirya sayar da dan wasan Belgium Eden Hazard, mai shekara 28, ga Real Madrid saboda idan Chelsea ta bari lokacin da kwantagarinsa ya kare a badi, hakan zai jawo mata cikas ta fuskar cinikayyar 'yan wasa, in ji jaridar Mail.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Koulibaly ya koma Napoli ne daga Genk a shekarar 2014

Manchester United ta fasa zawarcin dan wasan kungiyar Napoli, Kalidou Koulibaly, mai shekara 27, wanda ta taya fam miliyan 95, in ji (Gazzetto dello Sport journalist Nicolo Schira, via Sun) .

Tottenham tana neman dan kwallon Celta, Vigo Maxi Gomez, wanda ta taya fam miliyan 43, Spurs na son sayan dan wasan Uruguay din don ya rika maye gurbin Harry Kane idan bukatar hakan ta ta so, a cewar jaridar Sun.

Labarai masu alaka