Ada Hegerberg ce gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta 2019

Ada Hegerberg is the BBC Women's Footballer of the Year 2019

'Yar wasan kungiyar Lyon Ada Hegerberg ce masu sha'war kwallon kafa suka zaba a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta 2019.

Kyautar wadda masu sha'awar kwllon kafa a fadin duniya suka kada mata kuri'a ta zo ne bayan ta zura kwallo uku a gasar Zakarun Turai a lokacin da kungiyarsu ta lashe gasar.

"Kyautar nan babbar abin farin ciki ce a rayuwata," kamar yadda ta bayyana wa BBC.

'Yar wasan Denmark da kuma kungiyar Wolfsburg Pernille Harder ce ta zo ta biyu, yayin da 'yar wasan Australia da kuma kungiyar Chicago Red Stars Sam Kerr ta zo ta uku.

Sauran 'yan wasan biyar da suka fafata a gasar sun hada da 'yar wasan Japan da Lyon Saki Kumagai da kuma 'yar wasan Portland Thorns, sai kuma 'yar wasan Amurka Lindsey Horan.

'Yar kwallon Norway Hegerberg, wadda ta taba lashe kyautar a shekarar 2017, ta ce: "Abin farin ciki ne sake lashe gasar a karo na biyu."

Hegerberg ta kara samun shahara ne a bara lokacin da aka sanya ta a jerin 'yar wasan da za su fafata a gasar Ballon d'Or ta mata ta farko.

Kuma 'yar wasan ta yi fice wajen zura kwallo a raga.

A kakar shekarar 2017-18, ta ci yo wa Lyon kwallaye 53 ciki har da kwallaye 15 da ta zura a gasar Zakarun Turai.

Haka zalika a kakar bana, 'yar kwallon ta ci gaba da cin kwallaye inda ta zura kwallo 29 a wasa 33 - abin da ya sa kungiyarta lashe kofin lig na Faransa.

Labarai masu alaka