Chelsea na son £130m kan Hazard, Juve za ta karbo Pogba

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea za ta bukaci Real Madrid ta biya fam miliyan £130 idan har tana bukatar dan wasanta na kasar Belgium Eden Hazard mai shekara 28.

Sai dai kuma Real Madrid ta daraja dan wasan kan fam miliyan £88. (Sky Sports)

Manajan Chelsea Maurizio Sarri ya amince ya karbi aikin horar da Juventus bayan kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi watsi da bukatar. (Sunday Mirror)

Juventus kuma a shirye ta ke ta bayar da dan wasanta na gaba dan kasar Argentina Paulo Dybala mai shekara 25 da kuma dan wasan Brazil Alex Sandro domin karbo Paul Pogba daga Manchester United. (Sunday Express)

Manchester United kuma na dab da sayen dan wasan Ajax Matthijs de Ligt dan shekara 19, duk da Barcelona na son karbo dan wasan. (RAC1, via Metro)

Manchester City za ta biya Leroy Sane £150,000 a mako domin ya sake sabunta kwangilarsa da kulub din, a yayin Bayern Munich ke farautar dan wasan na Jamus. City za ta saka wa dan wasan mai shekara 23 kudi fam miliyan £100 idan har ya ki sabunta kwangilar shi. (Sunday Mirror)

Akwai yiyuwar David Silva ya gama taka leda a Manchester City bayan ba shi kwangilar shekara biyu ta makudan kudi a Qatar. (Sun ta Lahadi)

West Ham ta ce ta ba Barcelona £18m kan Andre Gomes wanda Everton ta karba aro a kakar da ta gabata. (Sunday Times)

Tsohon kocin Manchester United Sir alex Ferguson ya ce bai ji dadi da kulub din bai nemi shawararsa ba, inda ya ce kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya fi dacewa da Old Trafford ba Ole Gunnar Solskjaer. (Mail ta lahadi)

Dan wasan Najeriya Victor Moses zai koma Inter Milan daga Fenerbahce idan har Antonio Conte ya karbi aikin horar da Inter. (Football London)

Labarai masu alaka