Babu tabbas ko Neymar da Mbappe za su ci gaba da zama a PSG

Neymar da Mbappe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sha alakanta 'yan wasan biyu da Real Madrid

Kocin PSG Thomas Tuchel ya ce ba zai iya tabbatarwa ba ko Neymar da Kylian Mbappe za su ci gaba da zama a kungiyar har zuwa kakar badi, amma ya ce zai so su ci gaba da zama, kamar yadda kafar yada labarai ta Sky ta ruwaito.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane yana bakin kokarinsa wajen hana kaftin Sergio Ramos barin kungiyar, in ji (Marca - in Spanish).

Jaridar Marca ta Spaniya ta ruwaito cewa Liverpool da Man United da kuma wasu kungiyoyi a China suna nuna sha'awar daukar dan wasan mai shekara 33.

Dan wasan da Barcelona ke hankoron dauka Matthijs de Ligt, mai shekara 19, zai yanke hukunci kan makomarsa bayan kammala gasar Nations League, wadda kasarsa Netherlands za ta buga, a cewar (ESPN).

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan bayan Ajax ya bayyana cewa yana sha'war gasar Premier Ingila, kamar yadda gidan talabijin na ESPN ya bayyana.

PSG din kuma tana tattaunawa game da daukar James Milner na Liverpool, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa zai kare a karsehn kakar badi, in ji Le Parisien, via Metro.

Manchester City da Manchester United za su yi rige-rigen daukar dan wasan baya na Juventus Joao Cancelo mai shekara 25 idan sabon kocin kungiyar ya yadda ya sayar da shi - (Tuttosport, via Mirror).

Manchester City din kuma dai na kokarin daukar Youri Tielemans dan wasan Monaco, wanda aka yi wa kima kan fan miliyan 40, yayin da kuma Leicester City ke son daukar dan wasan wanda ke tare da su yanzu haka a matsayin aro, in ji jaridar Sun.

Labarai masu alaka