Champions League: A shirye nake tsaf - Harry Kane

Harry Kane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harry Kane yana fama da rauni ne a idon-sawunsa

Dan wasan gaban Tottenham Harry Kane ya bayyana cewa a "ya shirya yake tsaf" don tunkarar Liverpool a wasan karshe na Champions League.

Kane mai shekara 25 ya ji rauni ne a idon-sawunsa na hagu lokacin da ya fadi a wasan kusa da na karshe tsakaninsu da Manchester City ranar 9 ga watan Afrilu.

Tun farko koci Mauricio Pochettino ya ji tsoron cewa dan wasan ba zai samu damar sake buga wani wasa ba a kakar bana.

Sai dai dan wasan ya ce a shirye yake don shiga karawar ta ranar 1 ga watan Yuni.

"Ina jin zan iya bugawa don babu wata matsala zuwa yanzu," in ji Harry Kane.

Ya kara da cewa: "Na fara dawowa kan ganiyata tare da abokan wasana a karshen makon da ya gabata. A wannan makon kuma zan iya bakin kokarina in warware baki daya.

"Daga nan kuma ya rage ga kocinmu, ya duba kuma ya yanke hukuncin ko zai saka ni, amma ni dai kam yanzu garau nake ji na kuma a shirye."

Kane ya ci wa Tottenham kwallo 24 a baki dayan gasannin kakar bana duk da rashin buga wasanni na tsawon mako shida a watannin Janairu da Fabarariru saboda rauni a idon-sawunsa.

Labarai masu alaka