'Yan sanda sun kama 'yan wasan La Liga

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan sanda a kasar Spaniya sun kama mutane da dama game da zargin coge a harkar wasanni.

'Yan wasa na da da na yanzu da kuma jami'an kungiyoyin manyan gasar kasar guda biyu ne aka tsare.

"Wannan ya biyo bayan korafe-korafen coge kan wani wasan La Liga da aka buga a watan Mayu," in ji wani mai magana da yawun hukumomin gasar La Liga.

Daga bisani hukumomin sun kai rahotannin karin wasu cogen guda takwas ga 'yan sandan.

"Yayin kakar 2018/2019 ta La Liga an kai korafi guda takwas ga kwamishinan 'yan sanda kan zargin cogen wasanni a karamar gasar La Liga da kuma wasan sada zumunta tsakanin kananan kungiyoyi a Spaniya," a cewar hukumomin La Liga.

"Sannan mun aika da bayanai ga daraktan wasanni game da wasan kwallon kafa 18 bisa zargin cewa 'yan wasa a karamar gasa wadanda suka yi caca kan wasannin gasar tasu."

Bayanin ya kara da cewa: "Muna godiya ga 'yan sanda bisa babban kokari da suka yi na dakile gungun masu laifi da ke samun kudi da wasanni tun kafin a buga su.

"'Yan sanda sun nuna kwararewa da kishi ta hanyar kare tsarin da gasar La Liga ta shimfida wajen tsaftace gasar wasanni a Spaniya.

"La Liga za ta ci gaba da yaki da zambar wasanni a Spaniya."

Labarai masu alaka