Neymar zai 'dawo' Barca, Lukaku zai 'tafi' Inter Milan

Countinho da Dembele Hakkin mallakar hoto Soccrates Images
Image caption Countinho ya koma Barca a Janairun 2018, Dembele kuma a Agustan 2017

Rahotanni sun bayyana cewa Barcelona ta bayar da Philippe Coutinho ko kuma Ousmane Dembele ga PSG domin musaya, inda suke son a ba su Neymar, in jni Record.

Real Madrid ta bayyana cewa ta daddale fan miliyan 115 tare da Chelsea a matsayin kudin da za su biya kan Eden Hazard, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Romelu Lukaku ya yarda da rage albashinsa a Manchester United domin ya samu damar kowa wa Inter Milan a kaka mai zuwa, in ji Gazzetta dello Sport.

Kocin Man United Ole Gunnar Solskjaer ya sanya wa'adin zuwa karshen shekarar badi domin sayar da dukkanin 'yan wasan da ba za a ci gaba da tafiya da su ba a kulob din - Manchester Evening News.

Barcelona ta za ci gaba da zama da kocinsu Ernesto Valverde a kaka mai zuwa duk da rahotannin da ke cewa za a kore shi, a cewar jaridar Marca.

Tsohon kocin Chelsea Antonio Conte ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara uku don zama kocin Inter Millan har zuwa 2022. Shekara biyar kenan rabon da ya horar da wata kungiya a Italiya. (Tuttomercatoweb - in Italian).

Labarai masu alaka