Neymar zai 'koma' Barca, Man Utd za ta 'sayi' Adrien Rabiot

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarri ne ya jagoranci Chelsea ta lashe Kofin Europa a ranar Laraba

Kungiyar Juventus ta yi tayin biyan kocin Chelsea Maurizio Sarri fam miliyan 6.2 a yarjejeniyar shekara daya, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.

Sai dai a ranar Juma'a ne Chelsea za ta yanke hukunci ko kocin, mai shekara 60, dan Italiyan zai ci gaba da zama a kungiyar da ke birnin Landan, a cewar jaridar Express.

Manchester City da kuma Benfica suna tattaunawa kan makomar dan wasan Portugal, Joao Felix, mai shekara 19, in ji jaridar Sun.

Ana kyautata zaton cewa Manchester United ce za ta sayi dan wasan Paris St-Germain, Adrien Rabiot, mai shekara 24, a ranar 1 ga watan Yuli, kamar yadda kafar yada labarai ta (Mundo Deportivo - in Spanish) ta ruwaito.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana saran dan wasan Faransan Rabiot zai koma United din ne a farkon watan Yuli

Har ila yau United din za ta bar dan wasan Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 26, ya koma Inter Milan a kakar bana a kan fam miliyan 80, in ji Times.

Dan wasan Paris St-Germain, Neymar, mai shekara 27, yana son komawa tsohuwar kungiyarsa Barcelona a kakar bana, a cewar (Sport - in Spanish).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya koma PSG ne a shekarar 2017 daga Barcelona

Real Madrid ta shirya fara zawarcin dan wasan Chelsea, Eden Hazard, mai shekara 28, a kan fam miliyan 106, in ji jaridar Telegraph.

Hakazalika dan wasan Real Madrid da kuma Spain, Sergio Ramos, mai shekara 33, ya ce Hazard zai ba da gudunmuwa sosai idan ya amince ya koma Bernabeu a kakar bana, kamar yadda jaridar Star ta bayyana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hazard ya koma Chelsea ne daga kungiyar Lille ta Faransa a shekarar 2012

Chelsea tana so ta maye gurbin Hazard ne da dan wasan Barcelona, Philippe Coutinho, mai shekara 26, idan aka dage musu haramcin sayen sabbin 'yan wasa, in ji jaridar Mirror.

Ita kuwa Manchester City ta ki amincewa ne da tayin sayen dan wasan Jamus, Leroy Sane, mai shekara 23, wanda kungiyar Bayern Munich ta yi mata a kan fam miliyan 70, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Labarai masu alaka