Champions League: Yadda Liverpool da Tottenham ke shirin kece raini

Klopp da Pochettino Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta dauki kofin sau biyar, inda wannan ne karon farko da Tottenham ta zo wasan karshe a gasar

Tottenham za ta fafata da Liverpool a ranar Asabar a wasan karshe na lashe kofin zakarun Turai a Madrid.

Liverpool na fatan lashe kofin karo na shida, yayin da Tottenham kuma ke harin lashe kofin a karon farko a tarihi.

A bara Real Madrid ce ta haramta wa Liverpool lashe kofin a Kiev.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce sun koyi darasi daga rashin nasarar da suka yi a hannun Real Madrid a bara.

Kocin Tottenham kuma Mauricio Pochettino ya ce tsallakewa zuwa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, wani al'amari babba da zai iya faruwa da kulub din a tarihi.

Rabon da Liverpool ta lashe wani kofi tun 2012, tsawon shekara bakwai, yayin da Tottenham kuma tun 2008, shekara 11 da suka gabata.

Fafatawar lashe babban kofin na Turai na da matukar muhimmanci ga kungiyoyin biyu na Ingila.

Karon farko kenan da kofin gasar zai tafi Ingila bayan shekara 11. An shafe shekaru kofin na zuwa Spain.

Yadda 'yan wasan Liverpool ke atisaye

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana tunanin Liverpool za ta fara da Mohammed Salah bayan ya kauracewa wasan da ta lallasa Barcelona a Anfield saboda rauni
Hakkin mallakar hoto Stuart Franklin - UEFA
Image caption Kocin Liverpool ya tabbatar da cewa dan wasansa na gaba Roberto Firmino ya murmure, sai dai ya ki bayyana cewa ko zai fara da shi ko kuma a'a
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto David Ramos
Image caption Karo na biyu kenan a jere da Liverpool ke zuwa wasan karshe a gasar. Real Madrid ce ta doke ta a bara a birnin Kiev na kasar Ukraine.

Yadda Tottenham ke atisaye

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shi ne karon farko da Tottenham ta zo wasan karshe a gasar Zakarun Turan bayan ta lallasa Ajax da ci 3-2 a wani wasa mai cike da karya zuciya ga 'yan wasan na Ajax
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin Harry Kane ya bayyana cewa a shirye yake tsaf don buga wasan. Sai dai ya ce ya bar hukunci a hannun koci Mauricio Pochettino
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pochettino da Klopp babu wanda ya taba lashe kofi tun bayan fara aikin horarwa a Ingila, sai dai daga ranar Asabar wannan tarihi zai canza
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a buga wasan na bana a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid na kasar Sifaniya, wanda shi ne filin wasa na Atletico Madrid

Labarai masu alaka