Yadda Mesut Ozil ya angwance da amaryarsa

Shugaban Turkiya ne babban abokin ango Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Turkiya ne babban abokin ango

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya angwance inda aka yi bikinsa a Turkiya.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ne babban abokin ango a bikin na Ozil da aka gudanar a ranar juma'a.

Dan wasan na Arsenal mai shekara 30, ya auri amaryarsa ne tsohuwar sarauniyar kyau ta Turkiya Amine Gulse a wani babban otel a Istanbul na Turkiya.

Ma'auratan sun fara soyayya ne tun 2017, kafin su sanar da za su yi aure a watan Yunin 2018.

Ozil dai dan asalin Turkiya ne, kuma Bajamushe, inda yake wakiltar Jamus a kwallon kafa.

Ozil ya sanar da yin ritaya daga buga wa Jamus kwallo bayan ya suka kan wani hoto da ya dauka tare da shugaba Erdogan.

Hotunan bikin Ozil.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka