Real za ta gabatar da Hazard ranar Alhamis

Eden Hazrad Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid za ta gabatar da sabon dan wasan da ta sayo daga Chelsea, Eden Hazard gaban magoya bayanta ranar Alhamis.

Madrid ta dauko Hazard daga Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar, kan kudi da ake cewa zai kai fam miliyan 150.

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Portugal ya koma Chelsea daga Lille a 2012, ya kuma bar Stamford Bridge ne bayan da ya lashe manyan kofuna shida da buga wasa 352 ya kuma ci kwallo 352.

Hazard ya buga wa Chelsea wasa na karshe da kungiyar ta doke Arsenal a Baku da ci 4-1 ta lashe Europa League, inda ya ci kwallo biyu ya kuma taimaka aka ci daya a karawar.

Kawo yanzu Real ta dauki 'yan kwallo biyu kenan har da dan wasan Frankfurt mai ci wa kungiyar kwallaye Luka Jovic.

Madrid ta kasa taka rawar gani a kakar da aka kammala, inda Ajax ta yi waje da ita a gasar Champions League wadda ita ke rike da kofin.

Haka kuma Barcelona ce ta lashe kofin La Liga na bana, yayin da Real ta kare a mataki na uku, kuma kungiyar Camp Nou ce ta fitar da Real a Copa del Rey na kakar da ta wuce.

Labarai masu alaka