Ba mai magance matsalar Man United — Rooney

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wayne Rooney ya ce idan Manchester United za ta dauki Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ko Sergio Ramos ko kuma Gareth Bale ba za su iya magance matsalar kungiyar ba.

Rooney tsohon kyftin din United wanda ke taka-leda a DC United ta Amurka ya ce ko kusa bai da alamar cewar kungiyar ta Old Trafford za ta iya cin kofin Premier a badi.

Tsohon dan wasan Everton ya ce ba dabara ba ce a sayo dan kwallo daya ko biyu kan kudi fam miliyan 100, domin taimakawa wadanda suke kungiyar a yanzu haka.

Rooney mai shekara 33, ya ce kamata ya yi koci Ole Gunnar Solskjaer ya sayo 'yan wasa matasa 'yan fam miliyan 30 zuwa 40 masu hazaka da za su kawo ci gaba a United.

Ya kuma kara da cewar ''ba zai yi wu ka sayo Ranaldo ko Messi ko Ramos ko kuma Bale kan kudi mai yawa, kuma shekara biyu su kasa taka rawar da ka ke bukata, hakan hasara ne''.

Messi dan wasan Barcelona da Cristiano Ronaldo dan kwallon Juventus sun ci Ballon d'Or 10 a tsakaninsu.

Shi kuwa Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya lashe kofin duniya da na Turai da Champions League hudu.

Gareth kuwa shi ma ya ci kofin Zakarun Turai hudu ana kuma alakanta shi da cewar zai koma Old Trafford da murza-leda a bana.

Manchester United ta kare a mataki na shida a kan teburin Premier, hakan na nufin za ta buga gasar Europa Cup kenan ta bana.

Labarai masu alaka