Man Utd za ta sayar da De Gea

De Gea Hakkin mallakar hoto James Baylis - AMA

Manchester United ta nemi Paris St-Germain (PSG) ta biya ta fam miliyan 20 kafin ta sayar mata da golan Spain David de Gea, in ji jaridar Sun.

Shugaban kungiyar Benfica Luis Filipe Vieira ya ce Joao Felix, mai shekara 19, zai bar kungiyar a kakar bana a daidai lokacin da Manchester United ta fara zawarcin dan kwallon, a cewar jaridar Metro.

Sai dai Manchester City ta yi tayin biyan dan wasan fam miliyan 26, a cewar (Record - via Mail).

Kocin Arsenal Unai Emery ya fara magana da PSG kan Thomas Meunier, mai shekara 27, in ji Express.

Tottenham za ta fara neman dan wasan Fulham, Ryan Sessegnon, mai shekara 19, a kakar bana, in ji (Football.London).

Chelsea ta kara zage damtse wajen zawarcin dan wasan Bayern Leverkusen, Leon Bailey mai shekara 21, idan aka dage haramcin sayen sabbin 'yan wasan da aka sanya wa kungiyar, in ji jaridar Mail.

Labarai masu alaka