Super 6: Pillars da Rangers sun raba maki

Pillars Rangers Hakkin mallakar hoto Npfl

Kano Pillars da Enugu Rangers sun tashi 1-1 a wasan fitar da wadda za ta lashe kofin Firimiyar Najeriya na bana wato Super 6 da suka kara ranar Litinin a Legas.

Pillars din ta ci kwallo ne ta hannun kyaftin, Rabi'u Ali a bugun tazara a minti na 13 da komawa zagaye na biyu.

Rangers ta farke kwallon ne saura minti uku a tashi daga a bugun fenareti, bayan da aka yi wa Ifeanyi Egwim keta, kuma Godwin Aguda ya buga ta fada raga.

Da wannan sakamakon Kano Pillars ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki takwas, bayan da ta ci wasa biyu da canjaras biyu.

Ita kuwa Rangers ta hada maki biyar, bayan da ta ci wasa daya da canjaras biyu, aka doke ta karawa daya.

Ko a bara kungiyoyin biyu sun kara a wasan karshe a kofin kalubalen Najeriya, inda Rangers ta yi nasara da ci 4-2 a bugun fenareti.

Enyimba za ta iya hawa saman Pillars idan ta yi nasara a kan FC Ifeanyi Ubah.

Sai a ranar Laraba 12 ga watan Yuni za a karkare wasannin:

  • FC Ifeanyi Ubah da Enugu Rangers
  • Enyimba da Akwa United
  • Lobi Stars da Kano Pillars

Labarai masu alaka