Real za ta gabatar da Luka ranar Laraba

Luca Jovic Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid za ta gabatar da sabon dan wasan da ta dauko Luka Jovic gaban magoya bayanta a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

A ranar dan wasan zai fara sa rigar Real Madrid, sannan ya shiga fili ya yi wasa da tamaula, idan ya gama ya gana da 'yan jarida.

Madrid ta dauko Luka Jovic daga Eintracht Frankfurt kan yarjejeniyar shekara shida, wato kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2025 a Bernabeu.

Jovic ya koma Eintracht buga wasa aro daga Benfica a shekarar 2017, inda ya ci kwallo 17 a wasa 32 a Bundesliga da guda 10 da ya zura a raga a wasa 14 da ya buga a Europa League.

A watan Maris Real ta sanar da daukar Eder Militao daga Porto, kuma dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da ya koma Bernabeu tun karbar aiki karo na biyu a Bernabeu.

Haka kuma Real ta dauko Eden Hazard daga Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar, kuma a ranar Alhamis za ta gabatar da shi gaban magoya bayanta.

Labarai masu alaka