Griezmann zai koma Barca, Man U ta 'hakura' da Gareth Bale

Antoine Griezmann Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tuni Antoine Griezmann ya bayyana cewa zai Atletico Madrid a bana

Shugaban kulob din Atletico Madrid Miguel Angel Gil Marin ya tabbatar da cewa dan wasan gaba na Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 28, zai koma Barcelona a bana, kamar yadda kafar yada labarai ta Sport ta rawaito.

Sai dai a cewar jaridar Sun ta Ingila, Manchester United na son shiga cikin cinikin kuma a shirye take ta biya fan miliyan 95 din da Atletico Madrid ke bukata kan Griezmann din.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya musanta rahotannin da ke cewa yana tunanin tafiya hutu a karshen kakar wasanni mai zuwa, a cewar jaridar Independent.

Liverpool sun sake bayyana sha'awarsu ta sayen dan wasan gaba na Faransa da Lyon, Nabil Fekir, sai dai ba za su biya fan miliyan 53 da suka cimma yarjejeniya da Lyon a bara kan dan wasan mai shekara 25 ba, kamar yadda jaridar Le Progres ta bayyana kuma Daily Mail ta rawaito.

Rahotanni sun ce Daraktan wasanni na Juventus Fabio Paratici ya isa birnin Landon domin kammala kulla yarjejeniya da kocin Chelsea Maurizio Sarri, a cewar Calciomercato.

Sai dai jaridar Daily Mail ta rawaito cewa Chelsea ba za ta bar Sarri ya tafi ba har sai zakarun na Italiya sun biya kudaden da take bukata na katse kwantiraginsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dade ana alakanta Gareth Bale da Manchester United

Ana alakanta dan wasan baya na Chelsea Emerson Palmieri da komawa Juventus, sai dai dan kwallon na Italiya mai shekara 24 ya ce yana jin dadin zamansa a Stamford Bridge, kamar yadda Star ta rawaito.

Manchester United ta kawo karshen neman da take yi wa dan wasan Wales Gareth Bale - inda ta fasa taya dan wasan gefen na Real Madrid mai shekara 29, in ji jaridar Evening Standard.

Wakilin Matthijs de Ligt Mino Raiola ya gana da daraktan wasanni na Paris St-Germain Antero Henrique kan yiwuwar sayen dan wasan bayan na Ajax da Netherlands. Rahotanni sun ce kungiyoyin biyu na dab da cimma matsaya kan kudin da ya kai fan miliyan 66, a cewar RMC Sport.

Sai dai Express ta rawaito cewa Raiola ya musanta rahotannin cewa ya tafi Faransa domin tattaunawa da PSG kan cinikin De Ligt.