Manchester United ta dauki Daniel James

Daniel James Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta kammala daukar dan wasan tawagar kwallon kafar Wales, Daniel James daga Swansea City.

Dan wasan mai shekara 21, ya saka hannu kan kwantaragin shekara biyar da yarjejeniyar za a tsawaitata shekara daya, idan ya taka rawar gani a Old Trafford.

An ruwaito cewar United ta sayo dan kwallon kan kudi da zai kai fam miyan 15, kuma shi ne dan wasa na farko da koci Ole Gunnar Solskjaer ya dauko.

James ya fara daga karamar kungiyar Swansea, ya kuma ci kwallo biyar ya taimaka aka zura 10 a raga a wasa 38 da ya buga a 2018/19 a gasar Championship.

Labarai masu alaka