Pogba, Lukaku, Rakitic, Koscielny na kasuwar sayen 'yan wasa

Sarri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ta sahhale wa Sarri ya koma Juventus

Daraktan wasanni na Juventus Fabio Paratici ya je birnin London don ganawa da Manchester United kan dan wasa Paul Pogba mai shekara 26, in ji Sky Sports Italy, kamar yadda Sky Sports ta rawaito.

Liverpool ba ta da niyyar ci gaba da neman dan wasan tsakiyar Lyon kuma dan kasar Faransa Nabil Fekir duk da jita-jitar da ke yawo a kasarsa cewa zai koma kungiyar, a cewar Independent.

BBC ta fahimci cewa Chelsea ta amince kocinta Maurizio Sarri ya koma zakarun Serie A Juventus.

Dan wasan gaban Man United Romelu Lukaku ya yarda zai koma Inter Milan a wata yarjejeniya ta kusan fan miliyan shida a shekara ga dan wasan mai shekara 26 da kuma alawus-alawus har zuwa 2024, in ji Gazzetta dello Sport, kamar yadda Metro ta rawaito.

Manchester City sun jingine aniyarsu ta daukar dan wasan baya na Leicester City Harry Maguire, wanda aka yankewa farashi kan fan miliyan 90, a cewar Daily Mail.

Manchester United ce kan gaba wajen yunkurin daukar dan wasan kasar Portugal Bruno Fernandes daga kungiyar Sporting Lisbon, inda Man City da Liverpool ke neman dan wasan mai shekara 24, in ji Radio Rossonera, ta hanyar Jaridar Sun.

Borussia Dortmund na duba yiwuwar daukar dan wasan Arsenal mai shekara 33 Laurent Koscielny, wanda ka iya barin kungiyar a kowanne lokaci daga yanzu. Kamar yadda Daily Mail ta ce.

Ana sa ran Tottenham za ta dauko dan wasan tsakiyar Real Betis mai shekara 23 kuma dan kasar Argentina Giovani lo Celso da kuma Tanguy Ndombele mai shekara 22 dan kasar Faransa daga kungiyar Lyon.

Kudin da Tottenham za ta kashe kan 'yan wasan biyu zai zama shi ne mafi yawa da kungiyar ta taba kashewa wajen sayen 'yan wasa, in ji Mirror.

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce zai kyale Ivan Rakitic ya bar kulob din idan aka samu tayi mai kyau daga wata kungiya, in ji Cadena SER.

Arsenal na gab da daukar gola Markus Schubert dan kasar Jamus mai shekara 21 daga kungiyar Dynamo Dresden, a cewar (Independent).

Eden Hazard ya ce tsohon abokin wasansa kuma golan Real Madrid Thibaut Courtois ne ya taimaka wajen jawo hankalinsa game da komawarsa Madrid din, kamar yadda Football.London ta rawaito.

Labarai masu alaka