Ba na son lakabin matar shugaban kasa - Aisha Buhari

Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Twitter/Aisha
Image caption Umarnin na Aisha na zuwa ne kasa da wata guda bayan fara mulki a karo na biyu

Mai dakin Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce daga yanzu kada wanda ya kara kiran ta da lakabin 'Matar Shugaban Kasa', sai dai "Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady".

Aisha ta bayyana haka ne a wurin liyafar cin abinci da aka shirya domin girmama matan tsofaffin gwamnoni a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ta ce ta zabi a kira ta da "Matar Shugaban Kasa" ne don radin kanta duk da cewa ya haddasa rudani.

"Ni na zabi a kira ni da lakabin "Matar Shugaban Kasa a 2015 amma ina fatan za ku yafe ni bisa rudanin da ya haifar. Daga yanzu ina so a kira ni da Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady".

Sai dai kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Shugaba Buhari ya bayyana a 2014 cewa zai rushe ofishin First Lady idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Wannan ba shi ne karon farko ba da uwar gidan shugaban ke amfani da tarukan liyafa don isar da sako ba, ko dai ga 'yan kasa ko kuma mahukunta.

A watan Maris, jim kadan bayan mijinta ya lashe zabe a karo na biyu ta ja kunnen shugabannin jam'iyyar APC mai mulki kan rabon mukamai a wajen liyafar da aka shirya domin murnar nasarar mai gidan nata a Daura.

Mace mai jawo ce-ce-ku-ce - Sharhi daga Halima Umar Saleh

Hakkin mallakar hoto The Guardian
Image caption Maganganun Aisha Buhari na jan hanakalin jama'a da dama a shafukan sada zumunta

Ana yi wa Hajiya Aisha Buhari kallon mace mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan al'amuran da suka shafi mulkin mai gidanta.

A shekarar 2016 ne hakan ya fara fitowa fili bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa inda ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, suna hana ruwa gudu.

Ta yi zargin cewa ba a tafiya da wadanda suka sha wahalar kawo mijinta kujerar tasa wajen ba su mukamai, sai dai a dauko wasu can na nesa a ba su.

A wancan lokacin har ta yi ikirarin idan abubuwa ba su sauya ba to ba za ta mara masa baya a zaben 2019 ba.

Akwai kuma lokacin da ta soki jam'iyya mai mulki ta APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Amma wasu da dama sun daganta hakan da rashin samun nasarar dan uwanta da ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a APC din a zaben fitar da gwani.

Ga 'yan Najeriya da dama dai suna ganin abun da Aisha take yi bai dace ba, musamman ga tarbiyya irinta kabilar Hausawa da Fulani, amma a wani bangaren wasu kuma na ganin abun da Aisha ke yi daidai ne, domin gyara kayanka ne, wanda masu magana kan ce ba ya zama sauke mu raba.

Sai dai duk da sukar da take sha hakan bai hana ta yin gum da bakinta ba a duk lokacin da take zargin ana wani abu da bai dace ba a mulkin mijin nata.

Amma a baya-bayan nan ana ganin hotunan Aisha da mijinta na yaduwa a shafukan sada zumunta da muhawara da ke nuna yadda suke ji da juna.

Kuma ganin tun da aka fara yakin neman zabe har aka yi zabe ba ta yi korafi kan wani abu ba, ya sa wasu ke ganin kamar sun dinke barakar da ke tsakaninsu, (suna koren ganye).

Wace ce Aisha Buhari?

Hakkin mallakar hoto Twitter/Aisha

An haifi Aisha Halilu ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko.

Ta yi digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Public Admimistration, sai ta yi digirinta na biyu a kan harkokin kasashen waje.

Ta yi difloma a fannin kwalliya a makarantar koyon ado ta Carlton Institute da ke Windsor a Birtaniya, da kuma wata makarantar koyon gyaran jiki ta Academy Esthetique da ke Faransa.

Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari

Kafin maigidanta ya zama Shugaban Najeriya, tana da shagon gyaran jiki da kwalliya mai suna Hanzy Spa a jihar Kaduna.

Ta wallafa wani littafi na koyar da kwalliya da gyaran jiki wanda Hukumar da ke kula ta makarantun kimiyya da fasaha ta Najeriya ta sa shi a cikin manhajar da makarantun za su yi amfani da shi.

Aisha ta haifi 'ya'ya biyar da Muhammadu Buhari.

Labarai masu alaka