Abba Kyari ya haye next level, Auren Facebook ya lalata na gaskiya

Magajin Garin Daura Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption A farkon watan Mayu ne aka sace Magajin Garin Daura

A wannan makon a Najeriya, an ga abubuwa daban-daban da suka faru amma a fagen siyasa dai za a iya cewa kalmomin da aka fi ji ba za su wuce da sanata da tsaro da kotu da dai sauransu ba.

1) Yadda aka ceto surukin dogarin Buhari a Kano

A ranar Talata ne Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kubutar da Magajin Garin Daura Aljahi Musa Umar wanda wasu 'yan bindiga suka dauke watanni biyu da suka wuce.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano Abdullahi Haruna ya shida wa BBC cewa runduna ta musamman da ke yaki da masu garkuwa da mutane wato Operation Pupp Adr karkashin jagorancin Abba Kyari tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandan Kano ne suka kubutar da magajin garin.

Alhaji Musa Umar dai, surukin dogarin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne.

2) Buhari ya dakatar da batun kirkirar Rugar Fulani

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa ta dakatar da shirinta na kirkirar Rugar Fulani.

Mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter.

Matashiya

Dama dai tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na tsugunar da makiyaya ta hanyar gina masu "ruga," 'yan kasar na ciki da wajenta suka fara bayyana mabambantan ra'ayoyi.

Gwamnatin jihohi ma ba a bar su a baya ba, inda tuni gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya suka kekashe kasa cewa ba za su shiga wannan shiri ba.

3) Zanga-zanga a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu zanga-zanga sun rufe wata babbar hanya a Maiduguri ranar Lahadi 30 ga watan Yunin 2019 a lokacin wata zanga-zanga da aka yi don kira da a soke kungiyar 'yan sintiri masu yaki da Boko Haram ta CJTF.

4) Sanata Abbo ya nemi gafarar 'yan Najeriya

Hakkin mallakar hoto Elisha Abbo
Image caption Sanata Elisha Abbo na jam'iyyar PDP yana wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa ne

Dan majalisar dattijan wanda bayanai suka ambato shi cike da nadama a taron manema labaran da ya yi cikin shalkwatar jam'iyyarsa ta PDP da ke Abuja, ya nemi gafara, kuma ya ce a yafe masa.

Sanata Elisha Abbo, wanda ke wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa, ya ce "ba halina ba ne tozarta mata, don haka na yi nadama".

Faifan bidiyon dai ya tayar da kura da kuma janyo tofin Allah-tsine daga masu fafutuka da dumbin 'yan Najeriya har ma da fitattun 'yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta.

5) Takaddama bayan daura aure a Facebook

Hakkin mallakar hoto LUIS TATO
Image caption Matashin mai shekara 29 ya ce lamarin ya saka shi cikin tashin hankali

'Yan Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya suna neman wasu 'ma'aurata' bayan da suka daura aure a shafin Facebook.

Sanusi Abdullahi mai shekara 29 ya shaida wa BBC cewa wasa kawai yake da yarinyar bai san cewa karamar magana za ta zama babba ba.

6) An kashe 'yan Najeriya tara a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A Libya ana kamen 'yan ci-rani sannan a tsare su a cibiyoyin da gwamnati ke kula da su

'Yan Najeriya tara ne cikin akalla mutum 53 da aka kashe a harin da aka kai ta sama kan wata cibiyar tsare 'yan ci-rani da ke Libya, wanda duniya ta yi Alla-wadai da shi.

Binciken farko-farko na jami'an diflomasiyyar Najeriya da suka ziyarci cibiyar a yankin Tajoura ya tabbatar cewa 'yan kasar tara ne suka mutu a wannan hari, in ji ma'aikatar wajen Najeriya.

7) 'APC ce ta lashe zaben Osun'

Hakkin mallakar hoto OfficialAPCNg

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya ce Gwamna Adegboyega Oyetola ne ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

A watan Maris ne kotun sauraron kararrakin zabe ta ayyana Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben watan Satumbar shekarar 2018.

Daga nan ne sai Gwamna Oyetola ya daukaka kara.

Haka zalika a wannan makon ne aka fara zaman sauraron karar da dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kano Abba Gida-Gida ya shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe, inda yake kalubalantar zaben Gwaman Abdullahi Ganduje na APC.

8) Abba Kyari ya haye mukaminsa a karo na biyu

Hakkin mallakar hoto State House

Abba Kyari da Mustapha Boss sun sake zarcewa a mukamansu a karo na biyu, bayan da a ranar Juma'a Shugaba Buhari ya sanar da hakan.

Mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yada labarai Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a.

Ya ce nadin na su zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayun 2019, wato ranar da shugaban ya sha rantsuwar karbar mulki a karo na biyu.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya ciki har da 'yan jam'iyyar APC ke nuna adawa da ci gaba da kasancewar Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar.

Labarai masu alaka