Afcon: Amuneke da Tanzaniya sun raba gari

Emmanuel Amuneke Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Emmanuel Amuneke ya jagoranci Tanzaniya zuwa gasar Afcon ta farko tun 1980

Hukumar kwallon kafa ta Tanzania TFF ta tabbatar da sallamar Emmanuel Amuneke a ranar Litinin a matsayin kocin tawagar kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da tawagar Taifa Stars, wacce rabonta da shiga Gasar Cin Kofin Afirka tun 1980, ta kasa hayewa mataki na gaba bayan na sili daya kwale a Gasar Afcon da ake yi a Masar ta 2019.

Amuneke, wanda tsohon dan wasan tawagar Najeriya ne, ya zama kocin tawagar Tanzaniyan ne a watan Agustan 2018.

Hukumar kwallon kafa ta Tanzaniyar ta ce: "Hukumar kwallon kafa ta Tanzaniya da kocin tawagar kasar Emmanuel Amuneke, sun cimma wata yarjejeniya ta kawo karshen kwantiraginsa."

Hukumar ta ce za a nada sabon koci na wucin gadi bayan wani taron gaggawa da za ta yi ranar Alhamis, kuma shi zai jagorance su zuwa wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta CHAN da za a yi.

A farkon wannan watan ne Tanzaniya ta fara wasan neman shiga gasar CHAN inda ta fafata da makwabciyarta Kenya.

TFF ta kuma ce "tuni ta fara neman sabon kocin."

Amuneke, tsohon dan wasan tawagar Najeriya da Barcelona, shi ne mataimakin kocin matasan Najeriya 'yan shekara 17 da ta lashe kofin duniya a karo na hudu, wanda aka yi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a shekarar 2013.

Shekara biyu bayan nan, ya jagoranci tawagar Najeriya ta 'yan shekara 17 ta lashe gasar cin kofin duniya a karo na biyar da aka yi a Chile, hakan ya sa aka ga kwazonsa aka kara masa matsayi ya koma kocin matasa 'yan kasa da shekara 20 ta Flying Eagles.

A matsayinsa na dan wasa, shi jigo ne a tawagar Super Eagles, inda ya ci kwallaye a gasar cin kofin Afirka ta 1994 a Tunusiya inda Najeriya ta doke Zimbiya da ci 2-1 ta kuma lashe kofin karo na biyu a tarihi.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba