'Sai Madrid ta sayar da James za ta iya sayan Paul Pogba'

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid na son sayar da James Rodriguez domin ta hada kudi fan miliyan £150 wanda za ta sayi Paul Pogba da su, in ji Mail.

Haka zalika kungiyar Napoli ce ke son daukar dan wasan mai shekara 27 tare da Mauro Icardi mai shekara 26 daga Inter Milan, a cewar Goal.com.

Ita kuwa Bayern Munich tana jiran Leroy Sane dan shekara 23 ne a mako mai zuwa da ya yanke hukuncin ko zai taka mata leda ko kuma a'a, a rahoton jaridar Mail.

Kungiyar Rangers ta kasar Scotland ta karyata rahotannin da ke cewa kocinta Steven Gerrard zai koma Newcastle, inda ta ce labarin "kanzon-kurege" ne, kamar yadda Star ta ruwaito.

Kungiyar Fenerbahce kuwa ta shirya tsaf domin daukar Mesut Ozil mai shekara 30 daga Arsenal, a cewar Fanatik.

Kungiyoyin Arsenal da Manchester United da kuma Paris St-Germain suna son daukar Tiemoue Bakayoko mai shekara 24 daga Chelsea, inji RMC Sport.

Atletico Madrid ta kafa kwamitin ladaftarwa kan Antoine Griezmann, wanda ake tsammanin zai koma Barcelona kan fan miliyan £107, in ji Guardian.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Romelu Lukaku mai shekara 26 yana fatan koma wa Inter Milan kafin Manchester United ta kara da Inter Milan ranar 20 ga Yuli a wasan sada zumunta, Mirror ce ta ruwaito.

Arsenal na gab da daukar William Saliba daga Saint-Etienne kuma dan kasar Faransa, wanda ake sa ran zai kai fan miliyan £25, in ji (Evening Standard).

Liverpool tana hankoron ta ga ta hana Divock Origi barin kungiyar, yayin da shekara daya ce ta rage a cikin yarjejeniyarsa kuma kungiyar ta yi masa tayin yarjejeniya ta tsawon lokaci - Star

Ana alakanta dan wasan gefen kungiyar Ajax David Neres da koma wa Manchester United ko Everton, amma dan wasan ya ce makomarsa tana Ajax, a cewar rahoton Express.

Labarai masu alaka