Arsenal za ta dauki matashin dan wasan Faransa William Saliba

William Saliba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saliba (daga hagu) ya koma Saint-Etienne a 2016

Arsenal na dab da daukar dan wasan Faransa William Saliba kan fam miliyan 27 amma za ta mayar da shi aro ga Saint-Etienne.

Gunners za su biya wani bangare na cinikin dan kwallon mai shekara 18 da haihuwa, amma hakan ba zai shafi takaitaccen kasafin kudinsu na sayen 'yan wasa bana ba, wanda bai wuce fam miliyan 45 ba.

Saliba na daya daga cikin matasan 'yan baya da suka fi haskakawa a fagen tamaula.

Sai dai har yanzu Arsenal na neman dan wasan baya na tsakiya da za ta saya wanda zai iya taka mata leda nan take.

Saliba ya koma Saint-Etienne a 2016 kuma ba a sa ran bayyana yarjejeniyarsa zuwa Arsenal a 'yan kwanakin nan har sai an kammala komai.

Arsenal na kuma zawarcin dan wasan baya na Celtic Kieran Tierney, kuma tana fatan daukar dan wasan tsakiya da gefe.

A gefe guda kuma, kulob din ya nada tsohon dan wasansa Edu a matsayin mai kula da tsare-tsaren wasanni.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba