Fenerbahce na son Ozil, Barca na zawarcin Lindelof

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daraktan wasannin kungiyar PSG Leonardo ya ce ba zai iya tabbatarwa ba ko Kylian Mbappe zai ci gaba da zama kulob din ko kuma a'a, duk da cewa har yanzu Mbappe yana da shekara uku a cikin kwantiraginsa, in ji Le Parisien,.

Real Madrid ce dai kan gaba wajen neman dan wasan mai shekara 20, wanda ya koma PSG daga Monaco a Janairun 2018.

Barcelona ta mayar da hankalinta kan dan wasan Manchester United Victor Lindelof, bayan da rahotanni suka nuna cewa dan wasan Ajax Matthijs de Ligt da suke nema ya zabi ya koma Juventus, in ji jaridar Mundo Deportivo.

Dole Real Madrid ta biya kudin da ya fi na kowanne dan wasa tsada a duniya fan miliyan 162 idan har tana son ta dauki Paul Pogba daga Manchester United, a cewar Marca.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

KocinSheffield Wednesday Steve Bruce ya ce zai so ya tattauna da Newcastle idan suka nemi shi bayan da bayanai suka nuna cewa shi ne zai maye gurbin Rafael Benitez, in ji Chronicle.

Sai dai rahotanni daga jaridar Sun sun ce Rafael Benitez ya gargadi mataimakin kocin Manchester City Mikel Arteta da kocin Nice Patrick Vieira ka da su karbi aikin na horas da Newcastle.

Everton na sahun jerin kulob-kulob din da suke neman dan wasan Manchester City Fabian Delph, a cewar Sky Sports.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na son dan wasan gaba na Belgium Romelu Lukaku, ya yi watsi da bukatar Inter Milan ta sayan shi, ya ci gaba da zama a Old Trafford, in ji jaridar Sun.

Rahotanni sun ce Real Madridta yi wa Arsenal ragi domin ta sayi dan wasan gaba Mariano Diaz, mai shekara 25, kan fam miliyan 18, a cewar Star.

Fenerbahce na son daukar dan wasan Jamus Mesut Ozil a matsayin aro daga Arsenal, a cewarSky Sports.

Manchester United ta tuntubi Southampton domin neman sayen dan wasan Gabon Mario Lemina, kamar yadda Sky Sports ta rawaito.

Labarai masu alaka