Arsenal ta matsa kan Zaha da Malcom, babu inda Pogba 'zai je'

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal na son sayen dan wasan Barcelona Malcom, mai shekara 22, duk da cewa tuni Everton ta taya matashin dan kwallon fam miliyan 31.5, in ji jaridar Sun.

Tsohon dan wasan Liverpool Dean Saunders ya yi amannar cewa Ole Gunnar Solskjaer "ba zai wuce kakar bana ba" za a kore shi daga Manchester United, a cewartalkSPORT.

Sai dai har yanzu Solskjaer na da kwarin gwiwar shan-kan Manchester City wurin sayen dan bayan Leicester City Harry Maguire kan fam miliyan 75, in ji Daily Mail.

A shirye tsohon dan wasan Chelsea Diego Costa yake ya tattauna da Everton domin duba yiwuwar komowa Ingila saboda yana son barin Atletico Madrid, a cewarSun.

Dan wasanManchester United Juan Mata ya ce ya yi watsi da albashin fam 550,000 a duk mako daga kulob din Shanghai SIPG na China domin cigaba da zama a Old Trafford, in ji 90Min.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce babu wata barazana da za a yi masa da za ta sa ya sayar da Paul Pogba, a cewar jaridar Daily Mirror.

Juventus ta yi watsi da tayin Yuro miliyan 30 dagaEverton domin sayen matashin dan wasanta Moise Kean, in ji Tuttosport, da hanyar Sport Witness.

Tottenham na kara matsa lamba a yunkurinta na sayen dan wasan Real Madrid Dani Ceballos, mai shekara 22, a matsayin aro, in ji jaridar Mirror.

Arsenal za ta iya bayar da Calum Chambers, Carl Jenkinson, ko kuma Mohamed Elneny, domin musaya a cinikin da za ta yi da Crystal Palace kan Wilfried Zaha. Tuni Palace ta yi watsi da tayin Arsenal na fam miliyan 40, a cewar Mirror.

Labarai masu alaka

Karin bayani