Takaddama ta barke bayan da Griezmann ya koma Barcelona

France international Griezmann will have a release clause of 800m euros (£717m) at Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Griezmann ya koma Atletico ne daga Real Sociedad a shekarar 2014

Jim kadan bayan Barcelona ta bayyana daukar Griezmann a ranar Juma'a, Atletico Madrid ta mayar da martani da cewa kudin da Barcelona ta biya ya yi kadan.

Kulob din ya ce yuro miliyan 200 ne ya kamata Barcelona ta biya a matsayin kudin da yake cikin yarjejeniyarsa idan wata kungiya na son sayansa kafin kwantaraginsa ya kare.

Barcelona ta biya yuro miliyan 120 ne kan dan wasan, wanda a da yake a matsayin yuro miliyan 200 a lokacin da aka fara tattaunawa, in ji Atletico.

A ranar 1 ga watan Yuli ne dai aka rage farashin dan wasan daga yuro miliyan 200 zuwa 120.

"Mun yi imanin cewa kudin da aka biya bai cika ba domin kuwa an rufe tattaunawa da Barcelona kafin a rage farashin dan kwallon daga yuro miliyan 200 zuwa 120," in ji kulob din.

Dan wasan mai shekara 28 wanda ya lashe kofin duniya, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ciki har da Yuro miliyan 800 kudin da wata kungiya za ta dauke shi kafin yarjejeniyarsa ta kare.

Griezmann ya koma Atletico ne daga Real Sociedad a shekarar 2014 kuma ya ci kwallo 133 a wasa 256 da ya buga wa kungiyar.

Ya sabunta yarjejeniyarsa ta shekara biyar a watan Yunin shekarar 2018 ne, amma a watan Mayu ya bayar da sanarwar barin kungiyar a kakar bana.

Dan wasan shi ne na shida da ya fi tsada a duniya bayan Neymar, Kylian Mbappe, Philippe Coutinho, Joao Felix da kuma Ousmane Dembele.

Atletico ta taba yin karar Barcelona ga hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa FIfa game da yadda ta tuntubi Griezmann ba bisa ka'ida ba a watan Disambar 2017.

Sai dai Griezmann ya yi watsi da tayin da Barcelona ta yi masa a wancan lokacin.

Amma a farkon watan nan Atletico ta ce dan wasan da Barcelona sun wulakanta ta saboda yadda suka cimma yarjejeniya gabanin kungiyar ta sake shi.

Griezmann ne babban dan wasa na uku da ya bar kungiyar a bana.

Kuma kungiyar ta kammala gasar La Liga ne a matsayi na biyu - maki tara ne suka raba ta da Barcelona wadda ta kasance zakara.

Labarai masu alaka