Man Utd ta kara farashin Pogba, Juve na dab da sayen de Ligt

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A yanzu Real Madrid ce ta rage a sahun masu neman Paul Pogba

Manchester United ta kara fam miliyan 30 kan farashin da ta sanya wa Paul Pogba, a yanzu suna neman duk wanda zai saye shi ya biya fam miliyan 180. Miliyan 89 United ta saye shi a 2016, in ji Star.

Ita kuwa Juventus rahotanni sun ce ta kawo karshen zawarcin dan wasan na Faransa, inda a yanzu damar ta rage ga Real Madrid, a cewarDaily Mail.

Manchester United za ta iya komawa zawarcin dan wasan baya naMonaco mai shekara 18 Benoit Badiashile - wanda Wolves ma ke nema - idan suka kasa daukar dan wasan Leicester Harry Maguire, in ji L'Equipe, ta hanyar Express.

Akwai yiwuwar saiInter Milan ta biya kusan fam miliyan 90 idan har tana son sayen dan wasan Belgium Romelu Lukaku daga Manchester United a bana, in ji Telegraph.

Arsenal za ta nemi a biyata fam miliyan8.8 kan dan wasan baya na Faransa Laurent Koscielny, wanda ke son ya bar kulob din, kuma ya ki bin tawagar zuwa Amurka domin yin atisaye, a cewar London Evening Standard.

Wannan lamari ne kuma ya saArsenal ta sake komawa kan zawarcin da take yi wa dan wasan baya na Benfica Ruben Dias, mai shekara 22, in ji Daily Mail.

Juventus ta amince ta biya fam miliyan 63 domin sayen dan wasan baya na Ajax mai shekara 19 Matthijs de Ligt, a cewar De Telegraaf - in Dutch.

West Ham ta nemi a biyata fam miliyan 10 kan dan kwallon Equatorial Guinea Pedro Obiang, bayan da rahotanni suka ce Bologna da Sassuolona sonsa, a cewarSun.

Tottenham za ta taya dan wasan tsakiya na Leeds Kalvin Phillips, wanda aka yi wa farashi a kan fam miliyan 30, in ji Daily Mirror.

Har yanzuManchester United na sha'awar sayen Sean Longstaff daga Newcastle duk da cewa kungiyoyin biyu na da bambancin matsaya kan farashin dan kwallon na Ingila mai shekara 21, in ji Sky Sports.

Sai dai ana ganin farashin fam miliyan 50 da Newcastle ta sa kan Longstaff ka iya sa Manchester United ta kawo karshen zawarcin dan kwallon, a cewar ESPN.

Labarai masu alaka