Afcon 2019: Wa zai kori wani tsakanin Najeriya da Aljeriya?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Lahadi za a buga wasannin daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Masar ke karbar bakuncin gasa ta 32.

Za a fara ne da karawa tsakanin Senegal da Tunusia, can da dare a karkare da wasa tsakanin Aljeriya da Najeriya.

Mohammed Abdu ya yi mana duba na tsanake kan rawar da kasashen ke takawa a wasannin bana, musamma wasa tsakanin Aljeriya da Najeriya.

Najeriya ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyu da maki shida, biye da Madagascar wadda karonta na farko da ta je wasannin ta yi ta daya da maki bakwai.

A wasan zagaye na biyu ne Super Eagles ta doke Kamaru da ci 3-2 ta kuma kai karawar daf da na kusa da na karshe, inda ta yi gumurzu da Afirka ta Kudu ta kuma yi nasara da ci 2-1.

Ita kuwa Aljeriya ita ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki tara, sannan ta hadu da Guinea a wasan zagaye na biyu ta kuma ci 3-0, sannan ta cire Ivory Coast a bugun fenariti a karawar daf da na kusa da karshe.

Kawo yanzu Najeriya ta ci kwallo bakwai an kuma zura mata biyar a raga, ita kuwa Aljeria kwaya daya ne ya shiga ragarta, sannan ta ci guda 10.

Wasa tsakanin Aljeriya da Najeriya daya ne daga kasashen da suka fi haduwa da juna a gasar cin kofin nahiyar ta Afirka, saboda haka gumurzun na hamayya ne zai kuma yi zafi matuka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Najeriya tana da kofin Afirka guda uku da ta dauka jumulla, inda ta fara lashe shi a 1980 lokacin da ta karbi bakuncin wasannin.

A lokacin Super Eagles ta fafata ne da Aljeriya a wasan karshe inda ta yi nasara da ci 3-0 daga baya ta lashe gudu biyu a shekarar 1994 da kuma 2013.

Shekara goma tsakani Aljeriya ta lashe kofin nahiyar Afirka karon farko a lokacin da ta karbi bakuncin wasannin, inda Aljeriya ta yi nasara a kan Najeriya da ci 1-0 a wasan karshe.

Wannan shine karo na tara da kasashen za su fafata a tsakaninsu a gasar cin kofin nahiyar Afirka kadai, inda kowacce ta yi nasara a wasa uku-uku da canjaras biyu.

Wannan shi ne karo na 18 da kasashen biyu kowacce ke halartar wasan kwallon kafa mafi farinjini a Afirka, kuma wasa na karshe da suka kara a tsakaninsu shi ne wanda suka yi a 2010, inda Najeriya ta yi nasara da ci 1-0 a gasar cin kofin Afirka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sai dai sun fafata a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a watan Nuwambar 2016, inda Najeriya ta ci 3-1, a karawa ta biyu kuwa suka tashi 1-1 a Aljeriya a watan Nuwambar 2017.

A jadawalin wadanda ke kan gaba a taka-leda na hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Najeriya tana mataki na uku a Afirka ta 45 a duniya, ita kuwa Aljeriya tana ta 12 a Afirka ta 68 a duniya.

Sakamakon wasanni tsakanin Aljeriya da Najeriya a gasar kofin nahiyar Afirka

  • 22.03.1980 (wasan karshe) Lagos Nigeria 3-0 Algeria
  • 10.03.1982 (karawar cikin rukuni) Benghazi Algeria 2-1 Nigeria
  • 11.03.1984 (karawar cikin rukuni) Bouake Algeria 0-0 Nigeria
  • 23.03.1988 (wasan daf da karshe) Rabat Nigeria 1-1 (9-8 on penalties) Algeria
  • 02.03.1990 (karawar cikin rukuni) Algiers Algeria 5-1 Nigeria
  • 16.03.1990 (wasan karshe) Algiers Algeria 1-0 Nigeria
  • 21.01.2002 (karawar cikin rukuni) Bamako Nigeria 1-0 Algeria
  • 30.01.2010 (neman mataki na uku) Benguela Nigeria 1-0 Algeria
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Za a fara yin wasan daf da karshe ranar Lahadi tsakanin Senegal da Tunisia, ita dai Senegal bata taba daukar kofin Afirka ba, in banda mataki na biyu da ta yi a 2002.

Ita kuwa Tunisia ta lashe kofin Afirka karo daya a 2004 kuma shi kadai ne da ita duk da gasa ta 19 da take fafatawa, ita kuwa Senegal karo na 15 ake gumurzu da ita.

Senegal ce ta daya a jerin kasashen da ke kan gaba a tamaula a duniya ta 22 a duniya, ita kuwa Tunisia ita ce ta biyu a Afirka ta 25 a duniya.