Gareth Bale na dab da barin Real Madrid - Zinedine Zidane

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bale ya lashe kofunan Zakarun Turai hudu da La Liga daya a Real Madrid

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale na "dab da barin" kulob din, a cewar kocin kungiyar Zinedine Zidane.

Ba a sanya dan kwallon na Wales, mai shekara 30, a wasan da Real ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 3-1 a birnin Houston, na Amurka ba.

Da yake magana bayan wasan, Zidane ya ce: "Muna fatan zai barmu nan gaba kadan. Hakan zai fi kyau ga mu da kuma shi. Muna kokarin ganin ya koma wani kulob din.

"Ba ni da wata matsala da shi, amma wani lokacin ana daukar mataki saboda ya dace a dauka."

Bale, wanda ke da sauran shekara uku a kwantiraginsa a Real, ya lashe kofunan Zakarun Turai hudu tun lokacin da ya koma kungiyar kan fam miliyan 85 daga Tottenham a 2013 - wanda shi ne mafi tsada a lokacin.

A martanin da ya mayar kan kalaman na Zidane, wakilin Bale Jonathan Barnett ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Abin da Zidane ya yi abin kunya da takaici ne - ya nuna rashin mutuntawa ga dan wasan da ya taka muhimmiyar rawa a Real Madrid."

Ana alakanta Bale da komawa Manchester United da Tottenham, da Bayern da kuma kasar China.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba