Dani Ceballos: Arsenal ta aminci ta karbi aron dan wasan Real Madrid

Dani Cabellos na Real Madrid, ya taka wa Spaniya leda sau shida Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dani Cabellos na Real Madrid ya taka wa Spaniya leda sau shida

Arsenal ta cimma yarjejeniyar daukar aron dan wasan tsakiya na Real Madrid kuma dan Spaniya Dani Ceballos, domin taka mata leda a kakar 2019-20.

Ceballos, mai shekara 22, ya yi wa Real wasa sau 56 tun da ya koma can a shekara ta 2017, amma kuma ana ta baza jita-jitar tafiyarsa Arsenal da Tottenham a bana.

Ana sa ran tsohon dan wasan na Real Betis ya cike gurbin da Aaron Ramsey, wanda ya koma Juventus, ya bari.

Haka kuma Arsenal din na shirin sayen dan wasan baya na Saint-Etienne William Saliba, mai shekara 18.

Za a sayi matashin dan wasan na tawagar Faransa kusan fam miliyan 27, kuma zai koma Saint-Etienne aro a kaka ta gaba, kafin ya koma Arsenal din a 2020.

Saliba ya bayyana sha'awarsa ta tafiya Arsenal duk da cewa daga karshen nan Tottenham, ta nuna bukatar sayensa.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba