Kasuwar 'yan kwallo: Ina makomar Bale, Pogba, Messi, Rodriguez, da Dybala

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zidane ya nuna cewa ba ya so ya yi amfani da Bale a tawagarsa

Bisa ga dukkan alamu cinikin Paul Pogba mai shekara 26, na tafiya Real Madrid, daga Manchester United zai dogara ne ga barin dan wasan gaba na Wales Gareth Bale mai shekara 30 daga kungiyar ta Spaniya, kamar yadda (AS) ta ruwaito.

Bale, wanda ke karbar fam 550,000 a duk mako a Bernabeu, inda kwantiraginsa yake har zuwa shekara ta 2022, yana bukatar inda za a ba shi albashin da ya zarta na manyan 'yan wasa na duniya kafin ya bar Real Madrid, kamar yadda wata majiya ta kusa da dan wasan na Wales ta ce in ji (Sky Sports).

Bale zai samu akalla fam miliyan 20 na toshi banda albashinsa idan ya koma gasar China da wasa, kamar yadda jaridar Mail ta labarto.

Tottenham na shirin sake kashe makudan kudade a wannan makon domin kammala sayen dan wasan tsakiya na Real Betis kuma dan Argentina Giovani lo Celso, mai shekara 23, tare kuma da dan wasan baya na Fulham, na tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Ingila Ryan Sessegnon, mai shekara 19, in ji (Mirror).

Toby Alderweireld kuwa ana sa ran zai ci gaba da zama a Tottenham, duk da rade radin da ake yi cewa dan wasan bayan na Belgium mai shekara 30 zai koma Roma. A kwantiraginsa akwai dai sharadin cewa dole ne a sayar da shi idan wata kungiya ta taya shi fam miliyan 25 nan da ranar Alhamis, in ji (Telegraph).

Shi kuwa tsohon kociyan Chelsea Maurizio Sarri yana son dauko dan wasan bayan Tottenham ne, Danny Rose mai shekara 29 zuwa sabuwar kungiyarsa Juventus, kamar yadda (Mail) ta labarto.

Barcelona kuwa na shirin tattaunawa da Lionel Messi, mai shekara 32, domin tsawaita zamansa a kungiyar da karin wasu shekaru hudu kamar yadda (ESPN) ta ruwaito.

Hakkin mallakar hoto Quality Sport Images
Image caption Messi ya sha nuna aniyarsa ta yin ritaya a Barcelona

Mai yuwuwa Atletico Madrid ta mayar da hankalinta kan sayen gwanin dan wasan Real Madrid, dan Kolombiya, James Rodriguez, mai shekara 28, maimakon dan wasan tsakiya na Tottenham Christian Eriksen, na Denmark mai shekara 27, in ji (Marca).

Antoine Griezmann, mai shekara 28, ya ce kiris ya rage ya koma Manchester United, yayin da sabon dan wasan na Barcelona ke jaddada burinsa na yin wasa a kungiya daya tare da abokinsa na tawagar kasarsu Faransa kuma dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette, mai shekara 28, in ji (Goal.com).

Maganar barin dan wasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekara 26, kuma dan Leicester City, kusan da wuya duk da jita-jitar da ake yadawa cewa zai tafi Manchester United, in ji(Leicester Mercury).

Golan Manchester United David de Gea, mai shekara 28, na shirin sabunta kwantiraginsa wanda ya fi na da armashi, da a wannan karon ya kai na fam miliyan 117, wanda zai sa ya zauna a kungiyar har zuwa shekara ta 2025, sannan kuma yana son zama kyaftin a Old Trafford, kamar yadda jaridar (Manchester Evening News) ta labarto.

Ita kuwa Juventus a shirye take ta sayar da dan wasan Argentina na gaba Paulo Dybala, mai shekara 25, ga Manchester United a bazarar nan, idan dai an taya shi a farashin da ya kai fam miliyan 70 ko 90 in ji jaridar (Mail).

Labarai masu alaka